1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Turai ta soke yarjejeniyar EU da Amirka

February 12, 2010

Majalisar Turai ta dakatar da yarjejeniyar hadinkan bankuna tsakanin Turai da Amirka

https://p.dw.com/p/Lzpo
Majalisar kasashen Turai a StrassbourgHoto: AP

Kuri'ar da aka kada game da dakatar da yarjejeniyar tareda Amerika ta zama ta tarihi, wadda kuma a karshen ta masu adawa da yarjejeniyarda aka sani da suna yarjejejiyar Swift suka baiyan matukar farin cikin nasararda suka samu. Tare da babban rinjaye, yan adawar sun dakatar da yarjejeniyarda ake ta muihawara a kanta, da zata baiwa Amerika damar samun bayanai a game da musayar kudade da kai da komo da jama'a suke yi da bankuna a Turai. Yarjejeniyar an dakatarda ita ne kwanaki goma kawai bayan da ta fara aiki. Jim kadan kafin a kada kuri'u a majalisar, yan jam'iyar EVP ta masu ra'ayin yan mazan jiya, tayi kokarin ganin an dakatar da wnanan mataki, amma bata sami nasara ba. Martin Schulz, shugaban yan jam'iyar Social Democrats a majalisar ta Turai ya baiyana gamsuwar sa, inda kuma ya nuna cewar:

Ba ma babban kuskure ne ya samu a tsarin diplomasiyar Amerika ba, amma har suma shugabannin gwamnatocin kasashen TUrai sun yi kuskuren zaton cewar suna iya cimma yarjejeniya irin wnanan , su kuma gabatar da ita a majalisardokoki domin neman amincewar ta, ba tare da sun fahimci cewar irin wannan yarjejeniya a yadda take, ba zata sami amncewa ba.

Ta hanyar kin amincewa da wnanan yarjejeniya, majalisar ta Turai tayi amfani da sabon ikon da ta samu ne, inda godiya ta tabbata ga yarjejeniyar Lisbon, majalisarf tana iya hawa kujerar naki kan duk wani hadinkai tareda wasu kasashe, kamar Amerika.

Gwamnati a Washington tga baiyana rashin jin dadin ta a game da matakin kin amincewa da yarjejeniyarf musayarda labaran kan harkokin bankuna da majalisar Turai tayi. Gwamnatin Obama tana ganin hakan a matsayin wani hadari ga matakan hadin gwiwa na yaki da aiyukan tarzoma. Yanzu dai ana sa ran Amrika din zata karfafa neman hadin kai ne da kasashe da-dai na kungiyar hadin kan TUrai, maimakon da hedikwatar kungiyar kai tgsaye a Bruessels. AShugaba Barack Obama ya nunar a fili cewa:

Lokaci yayi da Amerika da Turai zasu sake komawa ga hadin da suka saba, domin fuskantar kalubalen wnanan karni na 21 gaba daya.

Sanarwar Obama yayi a bara cewar dangantaka tsakanin Amerika da Turai zata kasance dagantaka ce ta daidai wa daida, yanzu bata wuce shekara guda ba, amma tuni ta tsufa. Sghugaban na Amerika ya sha nunar da cewarf biranen Berlin da Paris da Bruessels, suma dai suna fuskantarf barazanar aiyukan yan tarzoma, kamaryadda Washington ko New York suke fuskanta. Yace

Saboda haka ne kasashen Turai da Amerika ya zama wajibi su kasance abokan hadin gwiwar juna, yadda zasu hada kai ga yaki da kungiyar al-Qaeda da magoya bayan ta.

Yan amajalisarf kasashen Turai duk da haka sun fi dora muhimmanci kan matakan kare asirin bankuna da masu huldodi da bankunan nahiyar fiye da hadin kai tsakanin asashen TUrai da Amerika.. Yan majalisar sun nunar da cewar ba zai yiwu a tafiyarda yaki kan aiyukan tarzoma ba tare da an kula da asirin jama'a da bukatun kare sirrin al'amuran su na yau da kullum ba.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Tijani Lawal