1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Turai za ta yi bincike akan zargin sansanonin Amurka a wasu kasashenta

January 18, 2006
https://p.dw.com/p/BvBi

Majalisar kungiyar gamayyar turai ta kada kuriar amincewa da gudanar da bincike akan zargin da akayi cewa hukumar leken asiri ta Amurka CIA ta gudanar da wasu sansanonin tsare wadanda Amurka take zargi da taaddanci a gabashin turai a asirce.

Kwamitin da aka kafa da zai gudanar da binciken zai kunshi wakilan jamiyyu arbain da shida ne na dukkanin jamiyyun dakeda mambobi a majalisar.

A farkon watan nuwamba ne dai na shekarar data wuce zargin na cewa Amurka ta rinka gudanar da wasu sansanoni na boye da take binciken yan Al-Qaeda a asirce a kasashen gabashin turai, wanda game da hakanne kungiyar kare hakkin danadam ta duniya Human Rights Watch tace tanada cikkakkun shedu da suka tabbatar da cewa lalle kam hukumar leken asirin ta Amurka CIA ta rinka kai wadanda ta kama a Afghanistan bisa zargin taaddanci zuwa kasashen Poland da Romania.

Sai dai dukkanin kashen biyu sun musanta wannan zargi.