1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makoki A Kasar Rasha

September 6, 2004

A yau litinin aka ci gaba da jana'izar mutanen da suka mutu a tabargazar nan ta murkushe matakin garkuwa da 'yan makaranta da aka yi a arewacin Rasha.

https://p.dw.com/p/Bvgj
Sojojin Rasha a matakin shawo kan garkuwar da ake yi da 'yan makaranta
Sojojin Rasha a matakin shawo kan garkuwar da ake yi da 'yan makarantaHoto: AP

A yau litinin ne aka ci gaba da jana’izar mutanen da suka yi asarar rayukansu a yayinda wasu da yawa daga cikinsu kuma ke ci gaba da kwanciya a asibiti rai hannun Allah. Dangin mutanen da ttsautsayin na zub da jini ya rutsa dasu suna cikin mawuyacin hali na rudami da rashin sanin tabbas a yayinda kasar ta Rasha gaba daya dake cikin makoki ita kuma duniya ta kadu a game da wannan masifa, wacce ba wanda ya san iyakacin barnar da ta haddasa. A hakika kuwa yawan mutanen da suka yi asarar rayukansu ya zarce yawan abin da mahukuntan Rasha ke bayarwa a hukumance. Sai dai kuma kawo yanzu babu wasu takamaimun alkaluma da aka bayar dangane da ainifin yawan mutanen da kaddarar ta rutsa da su ba. Ana fama da rahotanni masu jirkitaswa. Kuma kamar yadda shi kansa shugaba Putin ya tabbatar da kurakuran da jami’an kwatar da tarzomar suka caba, wadanda suka gane wa idanuwansu asbin da ya faru sun yi batu game da garajen da aka yi da kuma rashin basira wajen gabatar da matakin kai farmaki domin murkushe matsalar ta garkuwa da ‚yan makaranta a Beslan dake arewacin kasar Rasha. Mahukunta na daukar matakai iri dabam-dabam domin hana wa manema labarai binciko tahakikanin abin da ya faru kuma ba wani da yayi kurarin gabatar da mahawara domin tantance ainifin mafarin wannan rikici ta kafofin yada labaran Rasha. A makare shugaba Putin ya zarce zuwa yankin da matsalar ta faru domin ziyarar majiyyata dake kwance a asibiti sakamakon raunukan da suka samu daga rikicin. Kazalika Putin ya ki ya sadu da mazauna garin Beslan. A takaice shi kansa shugaban na Rasha yana cikin hali na rudu ne da rashin sanin tabbas. Wannan shi ne dalilin da ya sanya Putin ke ikirarin cewar kungiyoyin ta’adda na kasa da kasa na da hannu dumu-dumu a rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin Kaukasiya. Wadannan kungiyoyi masu zazzafan ra’ayi sune ummal’aba’isin kashe-kashe da tashe-tashen hankula a wannan yanki. Bisa ta bakin shugaba Putin ‚yan ta’addan sun wuce gona da iri sakamakon wannan mummunan mataki na rashin imani da suka dauka akan yara kanana suna masu mayar da farfajiyar makaranta tamkar wani dandali na sara da suka. Amma fa zai zama yaudarar kai da kai idan aka yi zaton cewar ‚yan ta’addan zasu daina cin karensu babu ba babbaka da zarar sojojin Rasha sun tattara nasu ya nasu suka fice daga Chechniya. To sai dai kuma a cikin bayanan da ya gabatar shugaba Putin ya ki ya tabo ainifin inda take kasa tana dabo domin kuwa yakin da ya ki ci ya ki cinyewa a Chechniya shi ne musabbabin wannan takaddama ta ‚yan ta’adda da sanadiyyar rayukan daruruwan mutanen da ba su san hawa ba ba su kuma san sauka ba. Bisa sabanin ikirarin da shugaban Rashan ke yi, wannan rikici ba an shigo da shi ne daga waje ba. Wannan rikici ne na cikin gida, wanda ya samu sakamakon matsalolin da Rashan ke fama da su da kuma fatali da aka yi da fafutukar neman ikon cin gashin kai da Chechniya ke yi. A dai halin da ake ciki yanzun ba abin da al’umar rashan ke bukata illa ganin an kyautata matakan tsaron lafiyarsu, amma ba kokarin dora wa al’ka’ida ko mayakan Chechniya alhakin hare-haren dake addabar kasarsu a cikin kwanakin goman da suka wuce ba.