1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MAKOMAR AIKIN KARE ZAMAN LAFIYA A KASAR KONGO

Yahaya AhmedMarch 3, 2005

Manazartan harkokin yau da kullum a kasar Jumhuriyar Dimukradiyya Ta Kwango na fargabar cewa, idan ba a dau matakan tabbatad da tsaro a kasar ba, to za ta iya fadawa cikin wani hali, wanda zai iya janyo wargajewarta tamkar kasa mai cin gashin kanta, kamar yadda aka samu a ksar Somaliya a cikin shekarar 1993.

https://p.dw.com/p/Bvct
Sojojin rundunar kare zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Jumhuriyar Dimukradiyya Ta Kwango.
Sojojin rundunar kare zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Jumhuriyar Dimukradiyya Ta Kwango.Hoto: AP

Har ila yai dai, kurar rikici ta ki lafawa a kasar Kwango. A ran talatar da ta wuce ne, dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke girke a wannan kasar, suka yi wani kazamin dauki ba dadi da wani rukunin `yan tawaye a jihar Ituri da ke arewa maso gabashin kasar. Farkon rahotanni dai na nuna cewa, dakarun kare zaman lafiyar sun harbe `yan tawaye 60 a musayar wutar da suka yi da su. Kamar dai yadda wata kakakin ofishin manzancin Majalisar Dinkin Duniyar a Kwangon, Eliane Naba ta bayyanar a birnin Kinshasa, sojojin kiyaye zaman lafiyar sun bude wuta ne don kare kansu daga afka musu da `yan tawayen suka yi, yayin da suke kokarin kare wasu `yan gudun hijira, fararen hula, da su `yan tawayen ke fatattaka. Ta kara da cewa:-

"Kusan `yan tawaye 50 ne akak kashe a wannan daukin. Dakarunmu na kare zaman lafiya biyu ne kuma suka ji rauni. `Yan tawayen dai sun matsa wa `yan gudun hijiran lamba, inda suke ta gallaza musu da azaba da kuma tilasa musu biyan kudaden haraji da ba su da tushe, da daim makamantan haka."

Tun makon da ya gabata ne dai, rikici ya barke a jihar ta Ituri, inda `yan tawayen suka yi wa wani rukunin dakarun Majalisar Dinkin Duniyar kwanton bauna, suka kashe 9 daga cikinsu. Masharhanta da dama na ganin hakan, wani babban cikas ne ga rundunar kare zaman lafiyar, wadda ta kunshi dakaru dubu b14 da dari 5. Da ma can dai, an sha yin korafi a kan girke wannan adadi na dakaru a kasar. Masu sukar lamiri na ganin cewa, matakin girke dakarun Majalisar dinkin Duniya a Kwangon, wanda aka dauka, aka kuma fara aiwatarwa tun 1991, shi ne mafi tsada daga cikin wurare 17 a duniya, inda ake gudanad da aikin wanzad da zaman lafiya, karkashin laimar Majalisar ta Dinkin Duniya. Kazalika kuma, an sha sukar irin halayyar da sojojin kare zaman lafiyar a Kwangon ke nunawa. An dai fi zarginsu ne da yi wa `yan mata fyade, da kuma sa wa `yan tawayen ido suna cin karensu babu babbaka a gabashin Kwangon.

Watakila, wannan mai da martani da dakarun kare zaman lafiyar suka yi, sanya wata alama ce ta nuna wa duniya cewa, lalle su ne ke jan akalar harkokin tsaro a yankin gabashin Kwangon. Kuma, zai iya kasancewa wani mataki ne na nuna cewa, lalle fa ya kamata a tsawaita wa’adinsu a yankin don hana tabarbarewar al’amura. A karshen wannan watan ne dai Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinin Duniyar, zai tattauna batun jan wa’adin rundunar zuwa wani lokaci can gaba.

Ofishin manzancin Majalisar Dinkin Duniyar a Kwangon dai na samun suka daga bangarori daban-daban, abin da ke janyo kira ga murabus din rukunin shugabancin wannan kafar ma gaba daya. Tuni dai, babban hafsan runudunar kare zaman lafiyar, Samaila Ilya, ya yi murabus a makon da ya gabata. Mai yiwuwa wasu manyan jami’an tawagar su bi sahunsa.

Rashin shawo kan rikici a gabashin Kwangon dai, ya shafa wa sunan rundunar kare zaman lafiyar kashin kaza. Ana zarginta kuma da janyo ambaliyar `yan gudun hijiran da ake ta kara samu a kasashen da ke makwabtaka da Kwangon. A cikin kasar Uganda kawai, an sami karin yawan `yan gudun hijira dubu 17 daga Kwangon tun farkon wannan shekarar, wadanda a halin yanzu ke jibge a gabar tafkin nan Lake Albert.