1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar gamayyar ƙasashe masu cigaban masana'antu

July 8, 2009

Shin ina ƙasashe masi cigaban masana'antu suka dosa?

https://p.dw.com/p/Ijf3
Hoto: AP


An samu canjin angizon ƙasashe a sassa daban-daban na duniya a cikin shekarun baya-bayan nan, inda ƙasashe kamarsu Indiya da China da Brazil suka shiga rukunin gaggan ƙasashe masu ci gaban masana'antu. Wani abin da ya ƙara taimakawa game da wannan sabon ci gaba shi ne rikicin kuɗin da aka fuskanta da taɓarɓarewar al'amuran tattalin arzƙin da ya biyo baya. Akwai dai alamun cewar aski ya fara ƙaratowa gaban goshi dangane da makomar gamayyar G8.

Bisa ga dukkan alamu dai gamayyar ta ƙasashen G8 ba zata iya tinkarar matsalolin dake addabar duniya ita kaɗai ba. Domin kuwa tuni ƙasashen da a da a kiransu wai ƙasashe masu matsakaicin ci gaban masana'antu suka kawo ƙarfi ta yadda ba za a yi ba tare da su ba. Babban misali a nan shi ne tarurrukan ƙolin tattalin arzikin da aka kira da farko a birnin Washington watan nuwaban da ya gabata da kuma London watan afrilun da ya wuce, sai da aka gayyaci ƙasashe kamar Brazil da Indiya da China da Mexiko da Afurka ta Kudu. Wato a baya ga ƙasashen G8 an hada da gamayyar ƙasashe biyar na G5. Sai kuma ƙarin wasu ƙasashe kamar Argentina da Australiya da Indonesiya da Saudi-Arabiya da Koriya ta Kudu da Turkiyya. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ita ce ta farko da tayi gangami a game da makomar gamayyar ƙasashen G8.

Bundeskanzlerin Angela Merkel gestikuliert am Donnerstag, 2. Juli 2009, waehrend ihrer Rede im Bundestag in Berlin.
Angela MerkelHoto: AP

Ta ce:"Gamayyar G8 an kafa ta ne sakamakon rikicin da aka fuskanta a zamanin baya. Gaggan ƙasashe masu ci gaban masana'antu sun haɗe waje ɗaya domin samar da wani dandali, inda za a riƙa tattaunawa a game da makomar tattalin arzikin duniya. Amma taron ƙolin L'Aquila zai bayyanar a fili cewar G8 kaɗai ba zata wadatar ba. Duniyar gaba ɗayanta tana bunƙasa ne tare. Kuma matsalolin da muke fuskanta a yanzu, kasashe masu ci gaban masana'antu ba zasu iya magance su su kaɗai ba."

Wannan kalamin na Angela Merkel na tattare da mamaki saboda ita ce kan gaba wajen adawa da karɓar ƙarin ƙasashe, kamar dai masu matsakaicin ci gaban masana'antu, a gamayya. A madadin haka shugabar gwamnatin ta Jamus ta ƙirƙiro abin da aka kira wai shawarar Heiligendamm, lokacin da Jamus ta karɓi baƙoncin taron ƙolin ƙasashe na G8 shekaru biyu da suka wuce. Wannan shawarar ta tanadi mayar da halartar zauren da kasashe masu matsakaicin ci gaban masana'antu suka saba yi a kowace shekara, a hukumance. Amma fa a yanzu al'amura sun canza a cikin ƙiftawa da Bisimillah sakamakon rikicin kuɗi na duniya ta yadda ya zama wajibi a ɗaga matsayin gamayyar domin ta zama ta ƙasashe 20 wato G20. Tun da su kansu ƙasashe masu ci gaban masana'antun, waɗanda sune ummalaba'isin rikicin na kuɗi basu da ikon shawo kan matsalar. Ga dai abin da Angela Merkel ke cewa:

Flashgalerie G8 Gipfel in L`Aquila, Italien, 2009
Mutum-mutumin shugabannin G8 a L'AquilaHoto: AP

Ta ce:"Na yi imanin cewar a sakamakon tarurruka na ƙasa da ƙasa masu tarin yawa da ake shirin gudanarwa a wannan shekara da kuma ta baɗi idan Allah Ya kaimu zamu samu kafar tantance fasalin da za a bai wa gamayyar. A yanzu muna da G8 da G20 da G5, amma a ganina wajibi ne lamarin ya ɗauki fasalin G20, wadda zata riƙa bitar matsaloli da neman shawo kansu. Saboda wannan gamayya zata ƙunshi gaggan kasashe ne dake da ƙarfin tattalin arzki."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Zainab Mohammed