1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar kuɗin Euro

June 17, 2010

A taronsu na Brussels shuagabannin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai zasu mayar da hankali ne akan makomar takardun kuɗi na Euro dake fama da tangal-tangal a halin yanzu

https://p.dw.com/p/Ntko
Kuɗin Euro na fama da tangal-tangalHoto: picture-alliance/dpa/DW

A sakamakon ɗimbim bashi dake kan wasu daga cikin ƙasashen gamayyar takardun kuɗin Euro da alƙaluma na jabu da suke gabatarwa da kuma sakosako da manufofinsu na kuɗi, takardun kuɗin na Euro suka shiga wani mawuyacin hali game da makomar darajarsu. A cikin watan mayun da ya wuce sai da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fito fili ta bayyana cewar Euro fa na fuskantar barazana.

"Idan har gamayyar takardun kuɗin Euro ta wargaje to kuwa ita ma ƙungiyar tarayyar Turai zata wargaje".

Wannan bayanin an ji shi ne daga bakin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel lokacin bikin miƙa lambar yabo ta Karlpreis ga P/M ƙasar Poland Donald Tusk a birnin Aachen tsakiyar watan mayun da ya wuce. Kuma ga alamu wannan lafazin ya burge ta matuƙa ainun, inda ta sake maimaita shi a majalisar dokoki ta Bundestag, kwanaki ƙalilan bayan haka...

"In har Euro ya gaza to kuwa Turai ma zata gaza"

Ba shakka, sigar lafazin tana da burgewa. Amma a fuskar tattalin arziƙi lamarin na da walakin, saboda lafazi ne da ba shi da ma'ana. Domin kuwa takardar kuɗi ba zata gaza ba ko wane irin suna ne za a laƙaba mata kuwa, walau Euro ne ko dala ko wani taken dabam. Matsawar da akwai mai amfani da ita a matsayin kuɗi, wannan takardar ta kuɗi ba zata gaza ba, sai dai kawai tayi asarar darajarta, in ji Jürgen Matthes daga cibiyar nazarin tattalin arziƙin Jamus:

"Dangane da masu zuba jari daga ƙasashen ƙetare faɗuwar darajar takardar Euro na ma'anar asarar kuɗi gare su. Ta wannan ɓangaren ana iya cewar hakan ya haifar da mummunan sakamako. Amma a ce wai takardar kuɗi ta gaza, abu ne mai wuyan fahimta."

To sai dai kuma ga alamu abin da shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ke nufi da lafazin nata shi ne wargajewar gamayyar takardun kuɗin Euro sakamakon ficewar wasu daga cikin membobinta daga ƙarƙashin inuwarta. Domin kuwa ba a iya korar membobin sakamakon wani laifin da suka aikata, in ji Jürgen Mathhes.

"Babu wata dokar da ta tanadi hakan. A ƙarƙashin sabuwar yarjejeniyar Lisbon, wadda ta fara aiki watan disemban da ya wuce kowace daga ƙasashen ƙungiyar na iya fita daga inuwarta. Amma fa wannan maganar ta shafi ƙungiyar tarayyar Turai ne kawai ba gamayyar takardun kuɗin Euro ba. A shari'ance dai hakan zata yiwu, amma a ɓangaren tattalin arziƙi wannan kuma wani lamari ne na dabam."

Abu ɗaya da ƙasa zata iya yi shi ne ta fice daga ƙungiyar tarayyar Turai, sannan bayan wasu daƙiƙu 'yan ƙalilan da sake komawa inuwarta, ta haka zata yi asarar wakilcinta a gamayyar takardun kuɗin Euro. Ta haka ƙasar da lamarin ya shafa zata samu ikon ƙayyade darajar takardun kuɗinta ta yadda zata iya shiga gasar ciniki ta ƙasa da ƙasa bisa sharaɗin cewar zata samu goyan baya daga ƙungiyoyin ƙodago domin rage yawan albashin ma'aikata. An fuskanci irin wannan alƙiblar a wasu ƙasashe na Asiya lokacin da yankin ya fuskanci matsaloli na kuɗi da tattalin arziƙi.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu