1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba kan makaman Amirka a Turkiya

Gazali Abdou TasawaAugust 15, 2016

Rahoton bincike na cibiyar Stimson mai fafutukar zaman lafiya a duniya, ya ce akwai fargabar yi wuwar fadawar makaman nukiliyar Amirka da ke Turkiya hannun 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/1JiJT
Incirlik Luftstützpunkt Archivbild 2001
Hoto: AFP/Getty Images/Tarik Tinazay

Sakamakon wani rahoton bincike da cibiyar ta Stimson da ke fafutukar zaman lafiya a duniya mai suna Centre ta wallafa a wannan Litinin din ya yi gargadin cewa akwai fargabar wasu makaman nukiliya kimanin 50 da Amirka ke ajiyarsu a filin jiragen saman sojoji na birnin Incirlik na Turkiya da ke kusa da kan iyaka da Siriya su fada a hannun Kungiyoyin 'yan ta'adda. Da ma dai an jima ana cece-kuce kan wadannan makaman nukiliya da Amirka ta ajiye a wanann wuri da ke da tazarar kilomita 110 kawai da kasar Siriya, kuma yinkurin juyin mulkin da aka yi a Turkiya a ranar 15 ga watan Yulin da ya gabata, ya sake farfado da wannan fargaba da aka jima ana yi kan dacewar zaman wadannan makamai masu hadari a wannan wuri. Rahoton binciken ya kara da cewa babu tabbas kan ko kasar Amirka za ta iya tabbatar da tsaron wadannan makamai idan yakin basasar da ake yi a kasar ta Siriya ya ci gaba da gudana.