1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Matakan Sake Gina Afghanistan

August 25, 2004

Jamus ba ta samu hadin kai daga sauran kasashen Kungiyar Tsaro ta NATO ba a kokarinta na sake gina kasar Afghanistan

https://p.dw.com/p/Bvh3
Shirye-Shiryen zabe a Afghanistan
Shirye-Shiryen zabe a AfghanistanHoto: AP

Duk wanda ya ba da la’akari sosai da yadda al’amura ke tafiya dangane da kasar Afghanistan tilas ne ya saka ayar tambaya a game da makomar kungiyar tsaron arewacin tekun atlantika NATO. Domin kuwa a wani lokaci can baya sakatare-janar na kungiyar Jaap de Hoop Scheffer yayi nuni da cewar kasar ta Afghanistan tamkar zakaran gwaji ce ga makomar wannan kungiya. A lokacin taron kolin shuagabannin kasashen kungiyar da aka gudanar a Istanbul a karshen watan yunin da ya wuce dukkan mahalarta taron sun amince akan bunkasa yawan sojojin kiyaye zaman lafiyar Afghanistan saboda kare zaben kasar da aka shirya gudanarwa a ranar tara ga watan oktoba mai zuwa. An yi wa shugaba Hamid Karazai alkawarin tsugunar da sojojin kiyaye zaman lafiya kimanin dubu uku da dari biyar, wanda ya gaza ainifin abin da shugaban ya bukata. Maganar da ba a shawo kanta ba a wannnan lokaci ita ce a game da kasashen da zasu ba da gudummawar wadannan sojoji. Amma kawo yanzu kasashen Spain da Italiya ne kawai suka yi alkawarin tura sojojinsu, wadanda gaba daya suka kama dakaru dubu daya da dari takwas kacal. Wannan tafiyar hawaniyar, irin shigenta ce ake fuskanta a game da tawagar sake gina kasar Afghanistan, wacce ta kunshi jami’an taimakon raya kasa da kuma kungiyoyi na farar fula. Gabanin taron kolin na Istanbul ana sha fama da cika baki a game da tura isassun jami’an sake ginawa wadanda zasu gudanar da ayyukansu a arewaci da kuma yammacin Afghanistan, sannan su kuma kasashen Jamus da Birtaniya da Italiya da Spain da Turkiyya da kuma Netherlands suka yi alkawarin ba da gudummawar sojoji domin kare lafiyar jami’an taimakon na farar fula. Amma fa tun tafiya ba ta je nesa ba kasashen Italiya da Spain da Turkiyya suka ta da kayar baya a lokacin taron kolin na Istanbul, suna masu kin amincewa da ba da gudummawar sojojin nasu. A karshen an cimma wani kwarya-kwaryan kuduri, wanda bai fayyace ainifin kasashen da zasu dauki nauyin ayyukan ba. Bisa ga dukkan alamu dai akasarin kasashen kungiyar ta tsaron arewacin tekun atlantika, NATO, ba su ga wani takamaiman dalili na tura sojojinsu zuwa Afghanistan ba, kuma hakan na daya daga cikin dalilan da suka sanya aka yi fatali da dukkan rokon da gwamnatin Jamus ta gabatar na neman hadin kai bisa manufa. Kasar ta Afghanistan na ci gaba da fama da rashin kwanciyar hankali, inda haulakan yakin kasar ke cin karensu babu ba babbaka, shi kuma shugaba Hamid Karazai, angizonsa ya takaita a fadar mulki ta Kabul kawai. Ta la’akari da haka bunkasa yawan sojojin kiyaye zaman lafiyar take da muhimmanci domin hana billar wani sabon yaki na basasa da karya alkadarin karuwar noman ganyen opium da ake amfani da shi wajen harhada hodar ibilis da kuma sake mayar da harabar Afghanistan wata mafaka ga ‘yan ta’adda.