1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar sabon kawancen 'yan adawa a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou DW Yamai/ MNAAugust 31, 2015

Kungiyoyin fara hula da ke kare mulkin demokradiyya a Nijar sun ce matakin da ministan cikin gidan kasar ya dauka keta haddin demokradiyya ne.

https://p.dw.com/p/1GOgK
Niger Niamey Opposition
Hoto: DW/M. Kanta

A cikin wata takarda mai lamba 2262 dauke da sa hannun ministan cikin gida Malam Hassoumi Massaoudou ne dai ministan yayi watsi da bukatar aminta da sabon kawancen mai suna FPR da 'yan adawan suka kulla a tsakiyar wata Agusta.

Ministan ya ce kawance ya tattara ne abubuwa barkatai da suka hada da kungiyoyin fararen hula da na 'yan siyasar da babu wata ka'idar da ke ci yanzu da za ta iya amincewa da sabon kawance na FPR, saboda hakan kawancen ba zai samu kyakkyawan tarbo ba daga hukumomin koli na kasar.

Sai dai tuni sanarwar ta ministan ke ci gaba da daukar hankalin jama'a musamman ma kungiyoyin da ke kare hakkin demokradiyya.

Fafutukar cimma manufar kare demokradiyya

Farfesa Djibril Abarchi shugaban kungiyoyin kare hakkin dan Adam ne da ake kira ANDDH, da ya ce:

"Babu inda doka ta ce jam'iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula da na kwadago an haramta musu su hada kansu, don idan ba haka ba yaya aka tafi babban taro na kasa? Domin bayan babban taron kasa ma ai an yi gwagwarmaya da yawa tsakanin jam'iyyun siyasa inda 'yan kungiyoyin fararen hula ne ko 'yan kwadago ne ko na jam'iyyun siyasa za ka ga kullum suna cewar abin da duk ya taba demokradiyya za mu tashi mu yi kokuwa a kan dole sai an mayar da demokradiyya, kawancen a siyasance ne ake yinshi saboda kokuwa ce ake yi domin cimma manufa."

Verfassungsgericht in Niamey Niger
Ko 'yan adawar za su garzaya kotun kare tsarin mulkin kasa?Hoto: DW/M. Kanta

Sai dai ra'ayi ya banbanta a tsakanin 'yan kungiyoyin na fararen hula. A yayin Djibril Abarchi ke ganin matakin ministan ya saba wa ka'ida, a cewar Abdou Maman Lokoko jigo a wasu kungiyoyin fararen hula matakin ministan ya dace, domin mutane na rudani ne kawai inda suke kwatanta ire-iren kawancen da aka kafa a da da suka hada da FRDD da CFD da CFDR ta baya bayan nan wacce gwamnatin da suke marawa ta yi yakin tazarce da ita a lokacin mulkin Tandja.

"Kawancen da an ka yi na CFDR akwai dalili, amma wannan da an ki yanzu babu dalili ko kadan. Iya sun yi niya suka ce sun yi kungiya wacce da karfi za su tilasta wa gwamnatin da jama'a suka zaba. In an yi wannan kawancen ne kawai don son mulki nan da nan kenan ba daidai ba ne."

Mabambamtan ra'ayoyi tsakanin masharhanta

Wannan banbancin ra'ayin dai na zuwa ne a yayin da kawancen ke ci gaba da kara samun karbuwa a fagen siyasa musamman ma ga masu adawa da manufofin gwamnatin kasar. Sai dai wasu masharhanta na ganin tamkar kawancen adawar yayi karambani da ya nemi samun izinin ministan cikin gida kuma dan jam'iyyar da ke mulki ba tare da la'akari da cewar sauran kawancen ba su taba samun izini daga ministan cikin gida ba.
To amma ga kungiyoyi ire-iren na su Abdu Mamman Lokoko kamata yayi ministan cikin gida ya gayyaci 'yan adawar domin jin dalilinsu na kafa sabon kawancen.