1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Tattalin Arzikin Jamus A Shekara Mai Zuwa

October 19, 2004

Ko da yake Jamus zata ci gaba da samun bunkasar tattalin arzikinta, amma ba zata cimma burinta na kashi 2% ba, kamar yadda masana na cibiyoyin nazarin tattalin arzikin kasar suka yi hasashe a cikin rahoton da suka gabatar ga gwamnatin yau talata

https://p.dw.com/p/BvfR

A cikin rahoton da cibiyoyin nazarin al’amuran tattalin arzikin Jamus suka bayar sun yi hasashen samun ci gaba iya gwargwado ga tattalin arzikin kasar a shekara ta 2005. To sai dai kuma duk da haka kasar zata zama tamkar ‚yar rakiya ce idan aka kwatanta da bunkasar tattalin arzikin sauran kawayenta a nahiyar Turai. Hasashen da cibiyoyin suka gabatar ya yi nuni da bunkasar kashi 1.5% na jumullar abubuwan da kasar ke samarwa a badi idan Allah Ya kai mu, a maimakon kashi 1.8% a wannan shekarar. Hakan kuwa ba ya nufin kawo karshen tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin Jamus ke fama da shi yau tsawon shekaru da dama. A lokacin da yake bayani Udo Ludwig daga daya daga cikin cibiyoyin tattalin arzikin na Jamus dake ba da wannan hasashe cewa yayi:

Matakai na garambawul da aka dauka ga tattalin arzikin kasar a karkashin ajenda 2010, musamman dangane da kasuwar kodago da tsarin jin dadin rayuwar jama’a abu ne dake ba da wani sabon jini ga tattalin arzikin Jamus. To sai dai kuma zai dauki wani lokaci mai tsawo nan gaba kafin a fara hangen tasirin wadannan matakai.

An dai samu dan ci gaba sakamakon sabbin ayyuka na gajeren lokaci da kuma wasu ‚yan kananan kamfanoni masu zaman kansu da aka kirkiro tun daga farkon wannan shekara, amma fa a daya hannun an samu karuwar yawan marasa aikin yi, inda masana tattalin arzikin suke hasashen karuwar mutane kusan dubu 300 da zasu rasa guraben ayyukansu a shekara mai zuwa. Wani abin da zai kara tabarbara lamarin kuma shi ne koma bayan cinikayya da ake fuskanta a cikin gida watakila saboda karancin kudin da mutane ke fama da shi a nan kasar yanzu haka. Kazalika, kamar yadda masanan suka yi hasashe, za a samu sassaucin cinikin ketare, sakamakon tafiyar hawainiyar da ake samu a kasashen Amurka da China, wadanda sune gaggan abokan burmin cinikin Jamus. Daya matsalar kuma ita ce ta fadi-tashin da ake fuskanta a game da farashin mai. Hauhawar kashi 10% na farashin man zai haifar da koma bayan kashi 0‘1% na jumullar abubuwan da Jamus ke samarwa a shekara. Amma kwararrun masanan sun hakikance cewar farashin man zai yiwo kasa zuwa dalar Amurka 37 akan kowace ganga daya a wajejen karshen shekara mai zuwa. Dangane da gibin kasafin kudi kuwa, kwararrun sun yi hasashen gibin Euro miliyan dubu 78, wato kwatankwacin kashi 3.5% na jumullar abin da kasar ke samarwa. Daukar tsauraran matakai na tsumulmular kudi ne kawai zai taimaka Jamus ta tsallake rijiya da baya domin cika ka’idojin KTT akan daidaita kasafin kudin kasa.