1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malalar mai a tekun Mexiko

June 12, 2010

Obama da Cameron za su tattauna akan matsalar kwararar mai a yankin tekun Mexiko

https://p.dw.com/p/NpG2
Zanga-zangar adawa da kwararar mai a tekun Mexiko da ke lahani ga muhalli da halittuHoto: AP

A ci gaba da lalubo bakin zaren warware matsalar tsiyayar man fetur da kamfanin BP na Birtaniya ya haifar a yankin tekun Mexiko, shugaban Amirka Barack Obama da Firaministan Birtaniya David Cameroun za su tattauna ta wayar tarho. Tattaunawar da shugabannin biyu za su yi a yau ta wayar tarho ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rashin daidaiton al'amura tsakanin ƙasashen biyu a sakamakon hasarar da kamfanin mai na BP ya haifar a tekun na Amirka. Sakataren makamashi na Birtaniya Chris Huhne ya jaddada cewa daidaita al'amuran BP ya dace da buƙatun ƙasashen biyu.

"Amirkawa na da hannun jari kashi 39 cikin 100 sannan 'yan Birtaniya na da kashi 40 cikin 100 a cikin wannan kamfani. Saboda haka muhimmin abu ne idan muka tabbatar da cewa BP ya ci gaba da aikinsa a matsayin wani kamfani mai ƙarfi."

Tuni dai gwamnatin Obama ta buƙaci kamfanin BP ya dakatar da biyan riba ga masu hannun jari a kamfanin har sai an warware matsalar da tsiyayar man ta haifar. A yayin da Birtaniya kuma ta baiyana goyon bayanta ga kamfanin, matakin da ya ɗaga darajar hannayen jarin kamfanin da kashi bakwai cikin ɗari. Yanzu haka dai kamfanin na BP ya ce ya fara samun nasarar shawo kan malalar da ɗanyen man ke yi a cikin teku na watanni biyu.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi