1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malalar sinadari mai guba a kasar Hungary

October 7, 2010

Ma'aikatan agaji na cigaba da kokarin shawo kan malalar guba a kasar Hungary.

https://p.dw.com/p/PXi8
Ma'aikatan agaji na kasar Hungarian ke kokarin kawar da sinadarin tabo mai guba a yankin Devecser.Hoto: AP

Kasar Hungary ta ce za ta shafe sama da shekara daya kafin ta kawar da bala'in tsiyayar guba daga wata masana'anta wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane hudu da jikata wasu da dama. Har yanzu akwai wasu mutanen da ba a ji duriyarsu ba bayan aukuar wannan balai.  Gubar dai na dauke ne da wani sinadiri da ka iya kone fatar jikin mutum. Jamiai sun kira wannan balai a matsayin irinsa mafi muni da kasar ta Hungary ta taba fuskanta.  Guba mai yawan kubik mita miliyan daya ne dai ya tsiyaya daga wani ma'aji na kamfanin karfen sanfulo da ke kusa da garin Kolontar, ya kuma malala zuwa wasu kauyuka bakwai da ke kewaye.  Kasar ta Hungary ta sa dokar ta baci a wasu jihohon kasar guda uku inda jamiai ceto ke aiki domin kawar da guban. An baiyana cewa gubar ta malale yanki mai fadin muraba'in kilomita 40 inda ake fargabar cewa zai iya danganawa da kogin Danube a kasar Romania wanda ya ratsa ta wasu kasashe uku a nahiyar turai. Kungiyar tarayyar turai a ta bakin kakakinta Joe Hennon tace a shirye take ta taimakawa hukumomin Hungary idan sun bukaci hakan domin kawar da illar sinadarin mai guba.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita :  Umaru Aliyu