1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malamai sun bukaci kwantar da hankali kan rikicin IPOB

Nasir Salisu Zango
September 14, 2017

Kungiyoyin matasa da malaman addini a Kano sun yi kira ga al'ummar da su kwantar da hankali kada su dauki doka a hannunsu domin wannan rikici manakisa ce kawai ga dimokradiyyar Najeriya..

https://p.dw.com/p/2k0LY
Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
Hoto: Getty Images/AFP

Tun lokacin da wannan rikici ya barke a wasu sassan kudu maso gabashin Nigeria da kuma birnin fatakwal 'yan kabilar Igbo mazauna Kano suka tsunduma cikin tashin hankali gami da fargabar yiwuwar daukar matakan ramuwar gayya a kansu lamarin da ya jefa su cikin zulumi.

Sai dai kuma kungiyar matasan arewa wadanda a baya suka baiwa 'yan kabilar Igbo wa'adin tattara yanasu yanasu su koma yankinsu. Sun bayyana cewar kada kowa a arewacin Najeriyar ya dauki doka a hannu domin kuwa wasu tsiraru ne kawai a can yankin suke kokarin yiwa dimokradiya manakisa, tare da tsokanar 'yan arewa domin hautsina kasar.

To amma duk da wannan ikirari na kungiyar matasan arewa galibin 'yan kabilar Igbo na zaune cikin fargaba musamman yadda ake yada hotunan mutanen da aka illata a yankin ta hanyoyin sadarwa, musamman ma facebook.

Malaman addinin musulunci ma a Kano sun tashi haikan domin hudubar kwantar da hankali tare da nuna illar daukar fansa akan wanda baiji ba bai gani ba. Sheikh Kabir Abdullahi Umar,malamin addinin musulunci ne mai wa'azi a Kano. Ya bayyana cewar musulunci bai yarda a afkawa mutane saboda dalilai na kabilanci ba.

Shettima shi ne shugaban kungiyar matasan arewacin Nigeria wanda ya ce a yanzu sun aike da wasikun korafi a kan abin da ke faruwa zuwa ga Majalisar Dinkin Duniya da sauran wuraren da ya dace domin neman a yi wa tufkar hanci idan kuma wasu na son barin kasa su tafi ba tare da an sami tashin hankali ba.

Zuwa yanzu dai jamian tsaro na ci-gaba da daukar matakai na tabbatar da ba a sami hatsaniya a Kano ba. Haka kuma hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta gayyaci shugabannin kafafen yada labarai domin neman hadin kansu kan kaucewa labarin da ka iya rura wutar wannan rikici.