1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta soma zaman makoki na kwanaki uku

Gazali AbdouTasawaNovember 23, 2015

Mali ta Soma zaman makoki na kwanaki uku Domin nuna alhini ga mutanen da suka mutu a cikin harin Hotel Radisson ta birnin Bamako a ranar Jumma'ar da ta gabata

https://p.dw.com/p/1HAUZ
Mali Geiselnahme Hotel in Bamako Befreiung von Geiseln
Hoto: Imago

A kasar Mali a wannan Litanin ne ake soma zaman makoki na kwanaki uku wanda hukumomin kasar suka ayyana domin nuna alhini ga mutanen da suka mutu a cikin harin ta'addancin da wasu 'yan bindiga suka kai a Hotel Radisson ta birnin Bamako a ranar Jumma'ar da ta gabata inda mutane 19 suka halaka.

Ko baya ga kasar Mali, a yau kasashen Afirka uku da suka hada da Senegal da Moritaniya da kuma Guinea suma sun shiga zaman makoki da sunan kara.

A share daya kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin tantance asali dama adadin mutanen da suka kai wannan hari na Hotel Radisson wanda kawo yanzu kungiyoyi biyu da suka hada da Al-Mourabitoune ta Mokhtar Belmokhtar dan asalin kasar Algeriya da kuma Kungiyar FLN ta masu da'awar samar da 'yancin yankin Macina na kasar ta Mali suka dauki alhakin kaddama da shi.