1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maliki yayi kira ga ´yan shi´a da su dakatar da kauracewa majalisa

November 30, 2006
https://p.dw.com/p/BuZa

FM Iraqi Nuri al-Maliki ya yi kira ga wakilan shi´a magoya bayan malamin mai tsattsauran ra´ayi Moqtada al-Sadr da su kawo karshen kauracewa majalisar dokoki. Bangaren ´yan shi´a da ya kunshi mutum 30 sun dakatar da goyon bayan su ga gwamnatin kawance ta al-Maliki inda suka janye ministoci 5 daga majalisar zartaswar don nuna adawar su da ganawar da FM yayi da shugaban Amirka GWB a Jordan. A taron na birnin Amman Bush ya bayyana Maliki da cewa shi ne shugaba na kwarai a Iraqi sannan ya jaddada cewar dakarun Amirka zasu saura a Iraqi har zuwa lokacin da gwmamnatin Iraqi ke so. Tattaunawar su ta bzo daidai da wasu tashe tashen hankula a birnin Bagadaza, inda jami´an Iraqi da na Amirka suka ce an gano gawawwaki 49 na wadanda aka yiwa kisan gilla a cikin sa´o´i 24 da suka wuce. A cikin wannan wata na nuwamba Amirka ta yi rashin sojoji fiye da 70 a Iraqi.