1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mandela yayi bukin cika shekaru 88 da haihuwa

July 18, 2006
https://p.dw.com/p/Buq7
A yau tsohon shugaban ATK Nelson Mandela ya cika shekaru 88 da haihuwa, a wani kwarkwaryar biki da yayi da iyalensa. Dukkan ´yan kasar ta ATK sun aikewa tsohon shugaban kuma gwarzo na yaki da mulkin nuna wariya sakon taya murna. Mandela wanda a hukumance yayi ritaya a shekara ta 2004 ya yi bukin ne a yau tare da dukkan danginsa a gidansu na gado da ke Qunu a can cikin lardin gabashin Cape. A cikin wata sanarwa da ya bayar shugaba Thabo Mbeki wanda ya gaji Mandela a shekarar 1999, ya yi fatan cewa Mandela wanda ake yiwa lakabi da Tata ko kuma Kaka a fadin ATK, zai tsawon rai don ya shaida yadda kasar zata bunkasa. A yau din ne kuma Mandela yayi bukin zagayowar shekara 3 da auren matarsa ta 3 Garcia Machel.