1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufar Jamus da Faransa ta samar da ci-gaban EU

October 27, 2010

Shugabar gwamnatin Jamus ta dage bisa cimma manufar samar da ɗorewar ci-gaban Ƙungiyar Tarayyar Turai

https://p.dw.com/p/PqYK
Angela Merkel a lokacin da take nuna wa majalisar dokoki damuwarta game da manufar samar da ci-gaban EUHoto: dapd

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta kare shawarar da Jamus da Faransa suka gabatar ta hukunta duk wata ƙasa ta Ƙungiyar Tarayyar Turai da za ta gaza cimma matsayin da ake buƙata daidai da yarjejeniyar samar da ɗorewar ci-gaban Tarayyar Turai. A cikin jawabin da ta yi ga majalisar dokoki a yau kafin Ƙungiyar Tarayyar Turai ta gudanar da taron kolinta a birnin Brussels a gobe Alhamis, Merkel ta ce Faransa da Jamus za su dage bisa aiwatar da tsaurara sharuɗa na aikin kuɗi ko da ma hakan zai buƙaci yin gyaran fuska ga yarjejniyar Lisbon da ke tafiyar da harkokin cikin gidan Tarayyar Turai. Shugaban hukumar zartarwar Ƙungiyar Tarayyar Turai, Jose Manuel Barroso ya yi wa ƙasashe mambobi tuni da cewar a taron na gobe za a mai da hankali ne akan hanyoyin samar da ci-gaban ƙungiyar. Tuni dai ƙungiyar ta fuskanci tsaiƙo game da wannan taro saboda adawar da wasu mambobin nata kamar ƙasar Luxembourg ke nunawa game da dakatar da haƙƙin kaɗa ƙuri'a ga duk wata ƙasa da za ta gaza cimma wannan matsayi.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Mohammad Nasiru Awal