1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

070909 Ausländerpolitik BTW

September 13, 2009

Yanzu dai shiru ake ji akan batun zaman baƙi da manufar ba da mafaka a yaƙin neman zaɓen ´yan majalisar dokokin Jamus ta Bundestag a bana.

https://p.dw.com/p/JeBH
Waɗannan nan dai wasu matan musulmi ne sanye da ɗan akwali a wata tashar safa dake birnin DuisburgHoto: AP

Wataƙila saboda a shekarun baya babu wani batu da yafi ɗaukar hankali kuma aka yi ta taƙaddama kansa a nan Jamus da ya kai na zaman baƙi cikin ƙasar. To sai dai manufofin jam´iyun sun banbanta kan wannan batu, wanda haka ke janyo kace-nace a yaƙin neman zaɓe.

Ganin yadda ake samun yawaitar tsofaffi a tsakanin Jamusawa ya sa batun zaman baƙi da shigar da su cikin harkokin yau da kullum zama wani batu na dindindin a fagen siyasar Jamus. Dukkan jam´iyun dake da wakilici a majalisar dokoki ta Bundestag na zayyana wannan batu a manufofinsu na yaƙin neman zaɓe, inda suke nuna amincewa da muhimmancin baƙi ´yan ƙaƙagida a cikin ƙasar kamar yadda aka ji daga bakin shugabar gwamnati Angeka Merkel.

"Tun shekaru masu yawa da suka wuce mu kan san cewa baƙi ´yan ƙaƙagida ni´ima ne ga ƙasarmu. Saboda haka tarayyar Jamus ƙarƙashin manufarmu ta karɓar baƙi mu ka samar da wani yanayi da za mu iya cewa muna maraba da waɗanda suka baƙwance mu da waɗanda suka shafe shekaru masu yawa a nan Jamus."

A cikin manufar kamfenta jamíyar CDU tana magana ne game da manufar ɗaukar baƙi yayin da take ƙin taɓo batun shigowar baƙi. Jam´iyar ta ce za ta yi ƙoƙarin bawa baƙin dake cikin ƙasar wani matsayi a cikin jama´a bisa sharaɗin cewa baƙin za su girmama dokokin ƙasar kuma za su nuna shirin zama tae da Jamusawa cikin girma da arziki.

Matsayin jam´iyun SPD da masu neman sauyi da FDP da kuma The Greens ya banbanta da na CDU da CSU. Ga waɗannan jam´iyu tuni Jamus ta zama wata ƙasa da baƙi ke sha´awar zama cikinta.

Ga jam´iyar masu sassaucin ra´ayi ta FDP manufar shigar da baƙi cikin jama´a na matsayin buɗe ƙofofin ƙasar ga duniya da kuma nuna juriya. Wannan dai shi ne kan gaba a manufofinta. Ita kuwa jam´iyar masu neman sauyi gargaɗi ta yi cewa bai kamata a kalli baƙin a matsayin waɗanda za a ci amfaninsu ne kaɗai ba. Ta ce hakan rashin mutunta bil Adama ne.

Yayin da CDU da CSU ke buƙatar baƙin da su rungumi Jamus da al´adunta da hannu bibiyu su kuwa sauran jam´iyu fata suke nunawa cewa ya kamata al´adun baƙin sun samu karɓuwa. Ra´ayoyin dukkan jam´iyun ya zo ɗaya cewa da sauran aiki gaba akan batun na shigar da baƙi.

´Yar SPD Andrea Nahles ta ce jam´iyarta ta fi ba da fifiko kan harkar ilimi ga baƙin.

"Fannin ilimi shi ne mafi muhimmanci wajen samun nasarar manufar shigar da baƙi cikin dukkan bangarorin rayuwarmu kuma ta haka za a tabbatar da samun cikakkiyar dama daidai wa daida a tsakani."

Ita ma jam´iyar The Greens tana ba da muhimmanci ga batun baƙin a yaƙin neman zaɓenta, inda take goyon bayan bawa baƙin damar taka rawa a dukkan fannonin zamantakewa da siyasar wannan ƙasa, musamman wajen ba su damar kaɗa ƙuri´a zaɓukan ƙananan hukumomi, kamar takwarorinsu baƙi daga sauran ƙasashen tarayyar Turai dake a wannan ƙasa.

Mawallafa: Heiner Kiesel/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmed Tijani Lawal