1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufofi uku na gwamnatin Buhari na tangal-tangal

November 25, 2016

Watanni kalilan bayan fara kassara 'yan kungiyar Boko Haram da masu sace mutane a Arewacin Najeriya, matsalolin tsaro da tattalin arziki da yaki da cin hanci na ci gaba da zama kalubale ga gwamnatin Muhammadu Buhari.

https://p.dw.com/p/2TGdC
Karikatur Buhari 1 Jahr im Amt
Hoto: DW

A cikin tsawon kasa da shekara guda kan mulki mahukuntan Abuja sun yi nasarar tabbatar da tasirinsu a kan hanyar kare matsalolin rashin tsaro walau na kungiyar Boko Haram ko ta barayin shanu da mutanen da suka dauki lokaci suna cin karensu har gashinsa. Sai dai kuma a wani abin da ke zaman alamun kurar yaki, sannu a hankali tarrayar Najeriya na sake fuskantar jerin matsaloli na tsaron da ke kunno kai a sassa daban-daban na kasar, wanda kuma ke neman share irin nasarar da hukumomin kasar ke tinkaho da su a can baya.

Kama daga yankin Niger-Delta inda tsageru suke rawar gaban hantsi, ya zuwa sashen Arewa maso gabashi da Boko Haram ke da sauran karfi, ya zuwa Arewa maso yammaci na tarrayar Najeriya inda barayin shanu da mutane ke neman zama saobbbin mammalakan al'umma, sannu a hankali lamura na neman subucewa ga Abujar da ke da fatan dorawa a cikin nasarorin baya amma kuma ke fuskantar turjiya ta ko'ina.

Nigeria Präsident Buhari empfängt befreites Schulmädchen Amina Ali
Shugaba Buhari ya fara ceto 'yan matan Chibok da ke hannu Boko HaramHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Fadar ta Abuja ta sake tura dimbin sojoji da nufin sake kwantar da hankula a jihar Zamfara da ta yi fama da kisa dama satar al'umma  a cikin makon da ke shirin karewa.Dr Garba Umar Kari da ke zaman wani masani a harkokin zamantakewa a tarrayar Najeriya, ya ce sake tada hankalin na nuna alamun barci a Abujar.

 

Batun sake tabbatar da tsaro cikin kasar da ta share shekaru tana fama da ta'addanci na zaman na kan gaba a cikin alkawuran zabe na shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi. Sai dai kuma sake hangen kurar rigingimun ta ko'ina na neman tada hankali na 'yan kasar da a baya suke dokin samun damar minshari a gidajen gadon. Malam Garba Shehu da ke zaman kakakin shugaban kasar ya ce gwamnatin ta sake yunkura da nufin kare kima da martabarta tsakanin 'yan kasar ga batun na tsaro.