1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manyan jami’an Ƙungiyar Haɗin Kan Turai sun gana da gwamnatin Sudan don tattauna batun yankkin Darfur.

October 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buhp

Manyan jami’an Ƙungiyar Haɗin Kan Turai sun gana da shugaba Hassan Omar al-Basir na Sudan a birnin Khartoum, a yunƙurin da suke yi na shawo kan gwamnatin ƙasar ta amince da girke dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya, da burin kawo ƙarashen yaƙe-yaƙe da annobar da ke addabar bil’Adama a yankin. Shugaban Hukumar Ƙungiyar, José Manuel Barroso, ya ce hukumar ta damu ƙwarai da halin da ake ciki, kuma za ta yi duk iyakacin ƙoƙarinta wajen ganin cewa an warware rikicin ta hanyar tuntuɓar juna.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya dai ya zartad da ƙudurin tura dakaru dubu 20 zuwa yankin don su maye gurbin dakarun sa ido na Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wato AU. Kawo yanzu dai, shugaba al-Bashir na watsi ne da shirin girke dakarun Majalisar Ɗinkin Duniyar, da cewa yin hakan ya saɓa wa ’yancin cin gashin kan ƙasar Sudan ɗin, sa’annan kuma wani yunƙurin ne da ƙasashen yamma ke yi na mamaye kafofin haƙo man fetur ɗin ƙasar.