1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manyan kasashe za su dafawa kasashen Afirka

March 19, 2017

Taron kasashe masu karfin masana'antu da aka kammala a karshen mako, ya amince da taimakawa bunkasa arzikin kananan kasashe, duk kuwa da zafin da zaman ya yi.

https://p.dw.com/p/2ZUm9
Deutschland | G20 Finanzminister Gipfel in Baden-Baden - Ausschnitt Gruppenfoto
Hoto: picture alliance/dpa/F. Kraufmann

Ministocin manyan kasashe masu karfin arziki na G20, sun bayyana sabbin dabarun zaburar da tattalin arzikin kasashen nahiyar Afirka, a wani taron da aka samu zafafan ra'ayoyi. Ministan kudi na Jamus, Wolfgang Schaeuble ya ce kasar Jamus mai masaukin baki, za ta baiwa nahiyar Afirka matukar fifiko musamman a bana.

Sanarwar bayan taron ta nunar da manufar da manyan kasashen suka cimma na karfafa harkokin saka jari da sauran fannonin inganta rayuwa a nahiyar ta Afirka. Akwai ma fatar bunkasa fannonin samar da ayyuka cikin batutuwan da aka amince da su a taron, kamar yadda wasu daga cikin wakilan kasashen Afirka a taron suka bayyana.

Wannan dai shi ne karon farko, da matsalolin nahiyar Afirka ke daukar hankalin ilahirin taron na manyan kasashen. Daga cikin kasashen Afirka dai, kasar Afirka ta kudu ce kadai ke da kujera a cikin gamayyar.