1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Margaret Thatcher dai itace macen farko data zama Firaministan ƙasar Birtaniya

January 31, 2010
https://p.dw.com/p/Lo7E
Tsohuwar firaministan Birtaniya Lady Margaret Thatcher ke tafi a wajen wani taron Jam'iyar su ta kwanzabatifHoto: AP

Margarate Thatcher dai  itace macen farko data zama Firaministan ƙasar Birtaniya kuma wasa wasa saida ta samu nasara a zaɓukan ƙasar har sau uku, woto dai sau uku tana zama Firaministan ƙasar a jere, tun daga shekarar 1979 da 1983 da kuma shekarar 1987.

An dai hafi MargarateThatcher ne a ranar 13 ga watan Oktoban 1925. kuma tayi makarantan Firamare na Kesteven da kuma sakandaren 'yan mata ta Grantham da kuma Somerville na jami'ar Oxford.

Kafin kuma ta shiga harkokin Siyasa a shekara ta 1959, ta kasance maibincike na kimiyyar kemistry daga shekarar 1947-54. A shekarar ta 1954 ne kuma ta zama cikakkar lauya. Daga shekarar 1970 zuwa 1974 kuma ta zama sakatariyar harkokin ilmi na Birtaniya.

A zamanin mulki ta ne dai Rhodesiya ta samu 'yancin kai ta zama Zimbabwe a shekarar 1979. Saidai wani abu daya ƙarawa Magarate Thatcher farin jin, shine nasasar da dakarun Indila suka samu a lokacin yaƙin tsibirin Falklands ashekarar 1982, abinda yasa Birtaniyawa suka sake zaɓen ta  azaɓen shekara ta 1983. Gama ka ɗan daga cikin abinda take cewa bayan sarandar da Sojojin Angentina sukayi wanda kuma ya kawo ƙarshen Yaƙin, inda take cewa: Ina son sheda maku sarandar da Sojojin Argentina sukayi, wanda ya baiwa Birtaniya nasara a wannan yaƙi na mallakan tsibirin falklands: A shekarar 1990 ne Magarate Thatcher ta sauka daga kan muƙamin Firaministan Birtaniya, kuma sunan mijinta Sir Denis Thatcher. Kuma tana da 'ya'ya biyu Sir Marka Thatcher da kuma Hon. Carol Thatcher da jikoki biyu mace da namiji. Yanzu haka dai Madam Thatcher tana da shekaru 84 a duniya.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Mohammad Nasiru Awal