1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maroko: Shekaru biyar ba harin ta'addanci

Jens Borchers/ MNAMarch 7, 2016

Kasar Maroko na amfani da matakai masu inganci da suka hada da kyakkyawar musayar bayanai wajen kare kanta daga hare-haren ta'addanci.

https://p.dw.com/p/1I8jT
König Mohammed VI. Marokko
Sarkin Maroko Mohammed na shidaHoto: Getty Images/AFP/A. Jocard

Shekaru biyar ke nan daidai da aka kai wani harin bam a tsakiyar birnin Marrakesh na kasar Maroko, inda aka kashe mutane 17 wasu da dama suka ji rauni. Tun wannan lokaci ba a sake kai wani hari a kasar ba, amma ana ci gaba da kame mutanen da ake zargi da kasancewa 'yan tarzoma, musamman magoya bayan kungiyar IS, da ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce na zama barazana. Hukumomin tsaron kasar da ake wa kallon masu inganci da kwarewar aiki, sun zama abokan huldar kasashen Turai ciki har da Jamus.

Abdelhak Khiame shi ne shugaban hukumar yaki da ta'addanci ta kasar Maroko da ke da sha'awar bayyana wa duniya kokarin da kasarsa ke yi a yaki da tarzoma, inda a kwanan nan ma'aikatansa suka cafke mutane 10 da ake zargi da ta'addanci.

Afghanistan Waffen
An kwace tuklin makamai daga hannun 'yan tarzomaHoto: DW/Z. Ahmady

"'Yan ta'addan suna da makamai iri daban-daban har da na guba. Kuma a karon farko sun so su yi amfani da wani yaro karami a matsayin dan harin kunar bakin wake. Suna da kyakkyawan horon aikin soja, suna dab da aikata ta'asar muka cafke su."

Matakai masu inganci na yaki da ta'adda

Ko da yake bai yi bayani dalla-dalla game da makaman masu guba ba, amma a fili take manufar bayyanar Abdelhak Khiame gaban manema labarai, wato nuna wa al'umma muhimmancin yakin da suke yi da ta'adda.

"Maroko na bin wasu kyawawan manufofi na hangen nesa. Suna kuma aiki da kyau. Tun bayan kafuwar babbar hukumar binciken ayyukan tarzoma, ta kame 'ya'yan kungiyoyi 24 na 'yan ta'adda."

Shekara guda ke nan da kafa wannan hukuma da ke da manufa shigen hukumar bincike ta tarayya a kasar Amirka wato FBI. Hukumar na da ma'aikata 400 tana da kayan aiki na zamani kuma a kullum tana musayar bayani da sauran hukumomin yakin da ta'addanci wato sojoji da 'yan sanda da Jandarma. Bugu da kari tana samun bayanai daga al'ummar kasa, abin da Abdelhak Khiame ya ce yana da matukar amfani.

Daga cikin nasarorin da hukumar ta yi har da tsegunta wa rundunar 'yan sandar kasar Faransa maboyar daya daga cikin 'yan ta'addar da suka kai hari birnin Paris.

Marokko Polizeiarbeit
'Yan sandan Maroko a bakin aikiHoto: DW/A. Laaraibi

Ba abin mamaki ba ne da a yanzu Maroko ta kasance sahun gaba a dandalin yaki da ta'addanci na kasa da kasa, inda ake musayar bayanai tsakanin kasahen duniya ciki har da Jamus da Amirka.

Amfani da tsoffin 'yan ta'adda don cimma manufa

Abdelhak Khiame ya nesanta addini da tarzoma. Sai dai ya san cewa kungiyar IS na amfani da kafafan yaudara don shawo kan matasan Maroko. Saboda haka ne gwamnati ke amfani da tsoffin 'yan ta'adda da suka taba zaman kaso kuma aka yi wa afuwa, don kira ga matasa da su guji ayyukan tarzoma, kamar Abderrazak Soumah tsohon mai tsattsauran ra'ayi da yanzu haka yake tallafa wa shirin Sarkin Maroko.

"Ina kira ga matasa da ke shiga kunhiyar IS da su kalle ni. Abin da kuke yi a yau, irinsa an yi sanda nake da shekaru 24. Bai tsinana min komai ba. Na rasa shekaru 30 na rayuwata a banza. Ban cimma komai ba, ko wa kaina ko abokai na ko kasa ta ba."

Ba wanda ya san ko wannan sakon zai shiga kunnen matasa, amma yana daga cikin dubarun yaki da ta'addanci da hukumomin Maroko suka bullo da su.