1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani a game da ´yancin Ossetiya da Abkhaziya

Yahouza, SadissouAugust 27, 2008

ƘasashenTurai da Amurika sun yi watsi da matakin Russia na amincewa da ´yancin Ossetiya da Abkhaziya.

https://p.dw.com/p/F5ob
Russia ta amince da ´yancin Ossetiya ta Kudu da AbkhaziyaHoto: AP


Al´umomin yankin kudancin Ossetiya sunyi shagulgulla , bayan da shugaban ƙasar Russia Dmitri Medvev, ya rattaba hannu a akan dokar da ta basu ´yancin ɓallewa daga Georgiya.

Jiya ne Majalisun dokoki da na Tarayya Russia, suka kaɗa kuri´ar amincewa da bukatar da yankin Ossetiya ta kudu da kuma Abkhaziya suka gabatar masu na ɓallewa daga Georjiya.

Amincewar ta shugaba Medvedev, ya nufi cewar  Russia tayi na´am, yankin kudancin Ossetiya da Abkhaziya,su ɓalle daga Georgiya,su kuma samu ´yancin kansu.

A yayin da yake bayyana dalilan da suka sa Russia ta amince, shugaba Dmitri Medvedev cewa yayi:Zaman sojojin Georgiya a yankin kudancin Ossetiya ya hadasa asara rayuwa rashawa masu yawa, saboda haka mataki mafi a´ala shine yankin ya samu ´yancin kansa.

Wannan al´amari ya jawo martani daga sassa dabam dabam na duniya.

Ƙasar France, dake jagorancin Ƙungiyar Tarayya Turai tayi tur da Allah wadai da shi.

Ministan harakokin waje Bernard Kouchner, yace EU zata shirya taron gaggawa domin tunani a game da hanyoyin ɓullowa rikici.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta bayyana matuƙar takaici tare da cewa: Haɗin kanda Russia ta baiwa yankin Kudancin Ossetiya da Abkhaziya domin su balle daga Georgiya mataki da za mu taba yadda da shi ba.

Mutunta iyakokin ƙasashe na daga gishishinƙan yarjeniyoyin ƙasa da ƙasa, wanda cilas ko wace ƙasa ta duniya ta bashi goyan baya.

A game da wannan batu, babu sassauci a kungiyar taraya Turai.

Shima kakakin gwamnatin Amurika cikin ɓacin rai yayi suka da kakkausar halshe da ƙasar Russia, ya kuma yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɗauki matakan ladabtarwa cikin gaggawa.

Itama Ƙungiyar tsaro ta NATO ta bayyana matakinan Russia a matsayin wani tubali na ginin fitina a yankin baki ɗaya.

Masu bi sau da ƙafa wannan rikici, da ya ɓarke tsakanin Russia da Georgiya, na fassara shi a matsayin wani saban yaƙin cyacar baka.

Sannan ya na da alamun jawo illolin masu yawa, a fagen siyasa da na diplomatiar duniya.