1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani akan jawabin Ahmadinejad

Tijani LawalApril 21, 2009

Jawabin Ahmadinajad a taron yaƙi da wariyar jinsi, inda yake zargin manufofin Isra'ila dangane da Palasdinu.

https://p.dw.com/p/HbQQ
Mahmoud AhmadinejadHoto: AP


Kamar dai yadda manazarta suka yi zato tun farko, shugaba Ahmadinajad na ƙasar yayi amfani da jawabinsa a zauren taron adawa da wariyar jinsi a Geneva domin bayyana kyamarsa ga Isra'ila. Sai dai kuma a can ƙasar Iran jawabin nasa bai shiga kannun rahotannin kafofin yaɗa labarai ba, saboda, ga alamu, akwai wasu matsalolin dabam da suka fi ci wa al'umar ƙasar tuwo a ƙwarya.

Ko da yake jaridar Iran Daily, rahoton da ta bayar yau talata, yana ɗauke ne da kanun "Wariyar Jinsi na tafiya ne kafaɗa-da-kafaɗa zaffar aƙidar yahudanci", amma fa ba jawabin ƙyamar Isra'ila da shugaba Ahmadinajad ya gabatar ne ya mamaye kanun rahotannin jaridun ƙasar Iran ba. Jaridun sun fi mayar da hankali ne kan kiran da yayi na soke ikon haua kujerar na ƙi a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya. Mai yiwuwa hakan na da nasaba da ƙaruwar da ake samu dangane da masu sukan lamirin furuce-furucen da shugaban ke yi da kakkausan harshe.

Bugu da ƙari kuma su kansu al'umar ƙasar sun amince da yadda gwamnati ke banbantawa tsakanin Yahudawa da masu zazzafar aƙidar mamayen Yahudanci. Inda ake banbantawa tsakanin manufofin Isra'ila dake da nasaba da aƙidar mamaye da kuma ainihin Yahudanci a matsayin addini. Waɗannan Yahudawa suna da cikakkiyar kariya a ƙasar Iran, wadda take ba su ikon buɗe makarantunsu har ma da wakilci a majalisar dokoki. Ana iya lura da wannan banbancin da la'akari da jerin gwanon da Yahudawan Iran suka yi domin bayyana adawarsu da hare-haren Isra'ila a zirin Gaza, inda kakakinsu Simak Morsathegh yake cewa:

Proteste Ahmadinejad Antirassismus Konferenz in Genf
Wakilai na ficewa daga zauren taronHoto: AP

"Mun hallara a nan ne domin mu bayyana adawarmu da take-taken gwamnatin Isra'ila mai zazzafar aƙidar mamayen Yahudawa da kuma nuna zumunci ga mutanen Palasɗinu da ba su san hawa ba ba su san sauka ba. Muna adawa da matakan sojan Isra'ila dake karkashe bayin Allah a Gaza. Kazalika muna fatan bayyanarwa ne cewar akwai banbanci tsakanin yahudanci da zazzafar aƙidar mamaye."

Abin dai dake jefa jami'an siyasa na ƙasashen yammaci cikin ruɗami shi ne yadda shugaba Ahmadinajad ke batu a game da kawar da Isra'ila daga doron ƙasa. Wannan maganar tana da sarkaƙiyar gaske fiye da yadda ake zato. Kalami na farko da aka ji daga bakin shugaban na Iran a game da Isra'ila a watan oktoban shekara ta 2005, kafofin yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa sun fassara shi ne da cewar: Wajibi ne a gusar da Isra'ila daga taswirar duniya.

Amma fa ainihin nassi na asali da kuma fassarar da cibiyar binciken al'amuran yankin gabas ta tsakiya mai goyan bayan Isra'ila ta gabatar cewa tayi: Wajibi ne a wayi gari, gwamnatin dake mamayar Ƙudus ta zama tarihi. Wato shugaba Ahmadinajad bai yi batu a game da kawar da Isra'ila ko halaka Yahudawa ba, maganar da yake yi shi ne kawo ƙarshen mamayen da Isra'ila ke wa birnin Ƙudus, wanda lamari ne mai raɗaɗi ga Musulmi.

Sai dai abin mamaki da ruɗami shi ne kasancewar shi kansa shugaba mai musunta ta'asar 'Yan Nazinhitler akan Yahudawa bai fito fili ya ce uffan a game da fassara kalaminsa akan kuskure da aka yi ba, a yayinda limamin limaman Iran Khmeinei da ministan harkokin waje Mottaki ke dagewa akan yi gyara ga wannan fassara.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita:Zainab Mohammed