1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Reaktionen Berlin

September 28, 2009

Yayin da jam´iyun Christian Unions da FDP ke cike da murna da farin ciki ita kuwa jam´iyar SPD cike take da baƙin ciki da alhini.

https://p.dw.com/p/JsFC
Guido Westerwelle na FDP da Angela Merkel ta CDUHoto: AP

Wannan dai shi ne a taƙaice halin da aka kasance ciki da sanyin safiyar yau a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, kwana guda bayan zaɓen ´yan majalisar dokokin ƙasar.

Ga jam´iyar Social Democrat wato SPD sakamakon zaɓen na zama wani abu mai ɗaci. Yawan ƙuri´u kashi 23 cikin 100 da jam´iyar ta samu shi ne irinsa mafi muni wanda a sakamakonsa ta rasa kashi ɗaya bisa uku na wakilanta a majalisar dokoki. An jiyo daga bakin babban sakatarenta Huberus Heil ya na cewa.

"Wannan mummunan kaye ne muka sha kuma za mu yi nazari kansa sosai. Wannan kuwa ya shafi kowa ba ´yan social democrat kaɗai ba. Dole mu sake lale wato abin nufi za mu yiwa jam´iyarmu sabon fasali a cikin shekaru masu zuwa. Za mu kasance ɓangaren ´yan adawa duk da cewa ba mu so haka ba. To amma wannan ƙawance ta CDU da FDP na buƙatar adawa ƙarfafa daga SPD."

Faɗuwar jam´iyar SPD ɗin dai bai zama wani abin farin ciki ga tsohon shugabanta Oskar Lafontaine ba. Lafontaine wanda yanzu shine shugaban jam´iyar ´yan neman canji, jam´iyarsa ta samu ƙarin ƙuri´u inda za ta samu wakilai 76 a majalisar Bundestag.

"Ba ma farin ciki domin raunin da SPD ta yi ya bawa CDU da FDP rinjaye. Da yawa daga cikin masu jefawa SPD ƙuri´a ba su fita zaɓe ba, abin da ya haddasa wannan sakamako kenan. Wani abi mai ɗaure kai shi ne yayin da muke cikin wani lokaci da duniya gaba ɗaya ke kira ga daidaita al´amura amma a nan Jamus wani gungu dake son tsuke bakin aljihun gwamnati ke son hawa kan mulki."

Wannan batun na rage kashe kuɗin gwamnati shi ne abin da FDP ta yi ta maimaitawa. FDP ta kasance wadda ta samu gagarumar nasara a zaɓen inda ta samu kashi 14.6 cikin 100 wato sakamako mafi kyau da ya bata matsayin jam´iya ta uku mafi girma a Jamus. Da sanyin safiyar yau ´ya´yan jam´iyar sun hallara a shelkwatarta daga cikinsu har da shugabanta Guido Westerwelle wanda ke hanƙoron samun muƙamin ministan harkokin wajen Jamus.

A tsakanin jam´iyun CDU da CSU ma an ga kyakyawan yanayi. Duk da cewa sun lashe zaɓen kuma shugabar gwamnati Angela Merkel za ta ci-gaba da ɗarewa kan wannan muƙami amma duk da haka jam´iyun na Christian Union sun yi asarar yawan ƙuri´u na kimanin kashi biyu cikin 100, musamman ma daga ɓangaren ƙawarta CSU ta jihar Baveriya. Duk da haka dai jam´iyun na begen samun ci-gaba kamar yadda aka ji daga bakin babban sakataren CDU Ronald Pofalla.

"Ya kamata a gaggauta tattauna batun ƙawancen wataƙila a cikin mako mai zuwa. Muna masu ra´ayin cewa ya kamata a kammala wannan tattaunawa cikin gaggawa. Burinmu shi ne a cimma wata yarjejeniyar kafa gwamnatin ƙawancen a cikin wata ɗaya."

Ita kuwa jam´iyar The Greens na matsayin wadda ta yi nasara kuma ta yi asara a lokaci guda. Ko da yake ta samu ƙarin ƙuri´u amma ba ta cimma burin da ta sa gaba na zama jam´iya ta uku mafi girma a Jamus ba.

Mawallafa: Bettina Marx / Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala