1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani ga afuwar da Fafaroma ya nema

March 20, 2010

Ƙungiyoyi suka ce afuwar da Fafaroma ya nema ga matsalar lalata da ƙananan yara bata isa ba

https://p.dw.com/p/MYL1
Fafaroma Benedikt na 16Hoto: AP

Ƙungiyoyin dake fafutukar kare ƙananan yara, waɗanda fada-fada a cocin Katolika na ƙasar Ireland suka tilasta yin lalata da su, sun bayyana cewar, afuwar da Fafaroma Benedict na 16 ya nema cikin wata wasiƙar daya aike ƙasar, bata wadatar ba. Ɗaya daga cikin ƙungiyoyin, wadda ake kira " ONE IN FOUR" ta ce Fafaroma bai nemi afuwa dangane da yadda hukumomin cocin suka hana ƙananan yaran da abin ya shafa yin magana ba, harma da ɗaukar matakin sallamarsu daga cocin baki ɗaya ba - a lokacin da suka yi ƙoƙarin kokawa ga ta'asar da shugabannin cocin suka tafka akansu. Akan hakane darektar ƙungiyar, Maeve Lewis ta ce, abin taƙaici ne cewar, Fafaromar ya sa ƙafa ya shure damar daya samu ta shawo kan matsalar nan data shafi yin aiki - da gangan da manufar cocin Katolika ta bada kariya ga waɗanda suka aikata laifin, abinda ta ce, yana kuma janyo hatsari ga rayuwar ƙananan yara.

Fafaroma Benedikt na 16 ya nemi gafara ga waɗanda al´amarin lalata da ƙananan yara ya shafa a cocin Katholika na jamhuriyar Ireland. A cikin wata wasiƙa da fadar Vatikan ta aikewa mabiya ɗarikar Katolika na Ireland, Fafaroma ya bayyana kunyarsa da nadama bisa wannan lamari na lalata da ƙananan yara yana mai cewa bishop-bishop na Ireland sun tabƙa kura-kurai wajen tinkarar wannan zargi. Ya ce fada-fada da ma´aikatan addini da aka kama da laifin yin lalata da yara za su fuskanci laifukansu a gaban wata kotu. Shugaban majami´ar Katolika a Ireland Sean Brady ya ce yana fata wasiƙar ta Fafaroma za ta maido da martabar cocin.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Yahuza Sadisou