1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani game da haramta amfani da bama-bamai

August 1, 2010

Paparoma ya nemi dukkanin ƙasashen duniya da su sanya hannu akan ƙudirin da ke haramta amfani da bama-bamai.

https://p.dw.com/p/OZYR
Hoto: AP

A yau Lahadi ƙudurin ƙasa da ƙasa da ya haramta amfani da ƙananan bama-bamai masu bazuwa ke fara aiki. Kawo yanzu ƙasashe 108 suka sanya hannu akan ƙudirin, yayin 38 ciki har da Jamus suka amince da aiki da shi.

Paparoma Benedikt na 16 ya nuna ɗoki da murna game da ci gaba da ƙudiri na ƙasa da ƙasa zai haifar. Shugaban ɗarikar katolika ta duniya yayi kira ga sauran ƙasashen da su rattaɓa hannu akan yarjejeniyar da ke hana ƙera makaman.

To sai dai manyan daulolin duniya da suka fi ƙera makaman, wato Amirka, da Rasha da kuma China ba su albarkaci wannan ƙuduri ba, wanda ya haramta amfani da nau'in ƙananan bama-baman masu yiwa fararen hula illa. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya bayyana ƙuduri a matsayin gagarumin ci-gaba a ƙoƙarin kwance ɗamaran makaman yaƙi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Mawallafi: Umaru Aliyu