1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan kafa gwamnatin hadaka a Jamus

Suleiman Babayo RGB
March 5, 2018

Jam'iyyun siyasa na Jamus na sahun gaba wajen mayar da martani kan kafa gwamnati hadaka da mambobin jam'iyyar SPD suka amince inda Shugabar gwamnati Angela Merkel za ta samu sabon wa'adi na mulki.

https://p.dw.com/p/2tiNL
Deutschland Ergebnis des SPD-Mitgliedervotums
Hoto: Reuters/H. Hanschke
Hannover Bundesparteitag Die Linke
Bernd Riexinger da ke jagoranci jam'iyyar LinkeHoto: picture alliance/dpa/P. Steffen

Ana ci gaba da samun martani mabanbanta game da matakin samun matsaya na kafa gwamnatin hadaka, watanni bayan zaben kasa baki daya da ya gudana. Jam'iyyun siyasa na kasar ta Jamus wadanda ke cikin majalisar dokoki na sahun gaba wajen mayar da martani kan kafa gwamnati hadakar da mambobin jam'iyyar SPD suka kada kuri'ar amincewa domin shiga gwamnatin tare da CDU/CSU da Shugabar gwamnati Angela Merkel ke jagoranci. Bernd Riexinger da ke jagoranci jam'iyyar Linke mai ra'ayin sauyi wanda ya ke ganin ba ta sauya zani ba:

"Godiya ga jam'iyyar SPD, inda Merkel za ta ci gaba da mulki. Maimakon gwagwarmaya bisa tabbatar da manufofi masu inganci ga kananan jam'iyyu, sai SPD ta mika kanta domin sake kafa gwamnatin hadaka. Ta raunana kuma ta dare sakamakon gwamnatin hadaka. Babu wani martani game da lamaru masu ci mana tuwo a kwarya da ake tsammani daga wannan gwamnatin. Ita gwamnatin hadakar ba ta da wani kargo."

A daya bangaren jam'iyyar Green mai hankoron kare muhalli tana gani akwai sauran aiki, kamar yadda shugabar jam'iyyar Annalena Baerbock ke cewa:

"Rashin tabbas a siyasarmu da ma kasashen Turai ya zo karshe sakamakon matakin mambobin jam'iyyar SPD. Duk da cewa akwai matakai masu inganci na gwamnatin hadaka, abin takaici shi ne abubuwa da aka bari. Jam'iyyun na hadaka ba su amsa hakikanin abin da ke faruwa a kasa ba, musamman na kalubale da ke gaba na sauyin da sauran kalubale kamar yaki da talauci tsakanin yara, abubuwan da suka zama gibi a yarjejeniyar gwamnatin hadakkar."

Yayin da jam'iyyu da suka saba shiga majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ke bayyana haka, ita kuwa jam'iyyar AFD mai kyamar baki wadda ta samu shiga majalisar dokoki kuma za ta kasance babbar jam'iyyar adawa ta ce lokaci kawai ake jira domin gwamnatin hadakar za ta rushe cikin kankanin lokaci, kamar yadda shugabar jam'iyyar Alice Weidel take gani:

Deutschland Alice Weide im Congresscentrum in Pforzheim
Alice Weidel shugabar jam'iyyar adawa, ta soki gwamnatin hadakaHoto: picture-alliance/dpa/S. Gollnow

"Mun fada wannan rana cewa a tarihin Tarayyar Jamus ba a taba samun lokaci mai tsawo game da kafa gwamnati ba sai a wannan lokaci. Haka ya nuna game da halin da jam'iyyu suke ciki. Sannan yana da wuya, saboda rashin iya tafiyar da lamura su iya cika muradun masu zabe."

Alice Weidel ta kara da cewa hadin gwiwar jam'iyyun na gwamnati CDU/CSU da SPD farin jinin da suke da shi tsakanin masu zabe na kara ja da baya. Sai dai galibi kasashen Turai masu tasiri kamar Faransa sun yi maraba da samun nasarar kafa gwamnatin ta Jamus bayan tsawon lokaci tun zaben watan Satumba na shekarar da ta gabata ta 2017. Kana akwai sakon taya murna na gwamnati hadakar ta Jamus daga bangarori daban-daban na duniya.