1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin ƙasashen Duniya

Zainab MohammedMarch 7, 2008

Martanin ƙasashen Duniya kan harin da aka kai a Birnin ƙudus a jiya.

https://p.dw.com/p/DKtT
Makarantar Birnin Kudus da aka kaiwa hari.Hoto: AP

Shugabannin ƙasashen duniya sunyi Allah wadan harin da aka kaiwa wata makarantar nazarin ilimin addini a birnin kudus,bayan da ƙungiyar masu tsattsauran ra'ayi na Hamas dake yankin Palastinawa ta ɗauki alhakin harin.

ƙalma mai tsauri na Allah wadan wannan harin na yankin Yahudawan ya fito ne daga Washington,wanda ke bayyana ɓacin rai dangane da yadda wasu Palastinawa sukayi jerin gwano a titunan zirin Gaza suna bayyana farin cikinsu da harin na jiya daya kashe yara matasa 8.

Kakakin fadar gwamnati ta White house Tony Fratto, ya fadawa manema labaru cewar abun bakin ciki ne ganin cewar mutane suna bukukuwa dangane da hallaka rayukan wasu.Sai dai yace abu mafi muhimmanci she ana cigaba da tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin biyu.

Jakadan Amurka a Majalisar Ɗunkin Duniya Zalmay Khalilzad,ya bayyana cewar wannan irin hali da ake ciki ne zai haifar da tsaaka mai wuya wa Majalisar wajen bada gudummowanta masu ma'ana,wajen tabbatar da cigaban yankin,sai dai waɗanda ke kawao cikas zasu dauki alhakin haka.

Tun a jiyan nedai shugaban Amurkan George W Bush da Babban Sakataren Majalisar Ɗunkmin Duniya Ban Ki Moon suka bayyana harin da kasancewa wani nau'i ne na mugunta.

Shima minisatn harkokin wajen Kasar Sweden Carl Bildt,bayyana harin yayi da kasancewa ta'addanci a ɓangaren 'yan hamas.Sai dai yayi kira ga bangarorin biyu da kada su yarda wannan sabon rikici ya haifar da tsaiko dangane kokarin da akeyi na samar da zaman lafiya a yankin.

Prime ministan Italiya Romano Prodi yayi kira ga Israela data cigaba da kokarin tattauna batun zaman lafiya da Paklastinu duk da wannan harin da aka kai a jiya.

Sanarwar data fito daga maaikatar harkokin wajen Turkiyya na fatan cewar irin wannan kiyayya da akan bayyana a fili,zai taimakawa bangarorin biyu wajen cimma zaman lafiya.

A nasu martanin shugaban ƙasar Faransa Nicholas Sarkozy da primiyan Britaniya Gordon Brown cewa sukayi,wannan yunkuri ne na haifar da tsaiko a kokarin da akeyi na cimma zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel,fadawa tayi cikin wani hali na rudani ,acewar kakakin gwamnati daga birnin Berlin,sakamakon harin makarantar birnin kudus din daya kashe matasa 8.

Jakadan Izrela a Majalisar Ɗunkin Duniya Dan Gillerman,yace babu yadda ƙasashen duniya zasu zauna shiru ayayinda ake aiwatar da miyagun ayyuka.