1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Aiman Alzawahiri a game da rikicin Lal Massajid na Islamabad

July 12, 2007
https://p.dw.com/p/BuGV

Shugaban ƙungiyar Alqa´ida, wato Ayman Alzawahiri, na hannun damar Usama Bin Laden, ya gabatar da wani saban jawabi, inda yayi kira ga ɗaukacin musulmin ƙasar Pakistan da su ɗauki fansa, a game da abunda da ya danganta da ta´adanci wanda sojojin gwamnatin ƙasar su ka aikata, a jan Massalaci na birnin Islamabad.

A halin yanzu dai, wannan massalaci ya shiga hannun dakarun gwamnatin Pakistan, bayan kwana da kwanaki, su na ɓarin wuta da yan takife.

Baki ɗaya mutane 80, wanda su ka haɗa da shugaban yan takifen Abdul Rashid Ghazi ,su ka rasa rayuka a cikin wannan rikici.

A jawabin nasa, Alzawahiri ya ce a yanzu matakin da ya rage kawai, shine na yaƙar shugaba Pervez Musharaf bil haƙi da gaskiya, ta hanyar jihadi, domin ƙwato yancin musulunci a ƙasar Pakistan.

Alzawahiri ya buƙaci Pakistanawa su bada goyan baya, ga ƙungiyar yan Mudjahideen ta ƙasar Afghanistan.