1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin duniya akan jawabin Netanyahu

June 15, 2009

Ana ci gaba da mai da martani daga sassa daban daban na duniya game da jawabin Netanyahu da aka kwatanta a matsayin hanyar samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa.

https://p.dw.com/p/IA4i
Firaministan Isra´ila Benjamin NetanyahuHoto: AP

Da yammacin jiya Lahadi fraministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi jawabin da aka daɗe ana dakonsa game da tafarkin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. Sai dai kuma ana ci gaba da mai da martani daga sassa daban daban na duniya game da wannan jawabi nasa da aka hango tamkar hanyar samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa.

Bisa ga dukkan alamu dai wannan jawabi na Netanyahu ba zai zama mafita daga rikicin Isra'ila da Falasɗinu kamar yadda shi kansa Netanyahu yayi fata ba. Dalilin haka kuwa shi ne amincewarsa da kafa ƙasar Falasɗinu wadda ba ta da makaman kare kanta da kuma haramta mata 'yancin yin amfani da sararin samaniya.

Netanyahu ya ce: "Za mu yarda da hakikanin shirin samar da zaman lafiya tare da kafa ƙasar Falasɗinu wadda ba ta da ɗamarar yaƙi a matsayin maƙwabciyar ƙasa ta Bani Yahudu muddin za a ba mu tabbacin kwancewa Falasɗinu ɗamarar yaƙi, tabbacin tsaro. A baya ga haka Falasɗinu ta kuma tabbatar da halalcin ƙasar ta Isra'ila."

A cikin jawabin da ya shafe rabin awa ya na yi firaministan ya kuma taɓo wasu muhimman batutuwa game rikicin Gabas ta Tsakiya da suka haɗa da samun bakin zaren warware matsalar 'yan gudun hijirar Falasɗinu a wajen iyakokin Isra'ila. Ya kuma nuna buƙatar dawwamar da birnin Ƙudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Sai dai kuma Falasɗinawa a nasu ɓangare sun miƙa buƙatar mai da gabashin birnin Ƙudus a matsayin babban birnin ƙasar Falasɗinu. Gwamnatin Falasɗinu da Mahmoud Abbas ke jagoranta ta yi suka ga waɗannan kalamai na Netanyahu tana mai cewa wannan jawabi nasa na zaman karan tsaye ga tafarkin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. Rafiq al-Hussein babban jami´i na shugaban Falasdinu ya bayyana jawabin Netanyahu tamkar shelar shiga yaƙi da duniya baki ɗaya.

Yace: "Ni dai a nawa raayi abin da ya ke nufi shi ne Falasɗinawa ba za su samu kasa mai cin gashin kanta ba.saboda cewa ya shimfida sharuɗɗan da ba za su samu karbuwa ba.Wannan jawabi nasa ba ma yana zaman shelar shiga yaƙi da Falasɗinawa kaɗai ba ne a'a amma har da duniya baki ɗayanta. Buƙatar da duniya ta mika wa Isra'ila ita ce kafa 'yantattun ƙasashe guda biyu a matsayin mafita, inda falisdinu za ta kasance a gabar yamma da kogin Jordan da zirin gaza hada da birnin Kudus. A baya ga haka akwai buƙatar magance matsalar 'yan gudun hijira. Amma ga shi yau Netanyahu yayi watsi da waɗannan buƙatu. Saboda haka ba ma Falisɗinu da Larabawa kadai ne za su ƙalubalance shi ba. Sauran ƙasahen duniya ma za su ƙalubalance shi."

Ƙungiyar tarayyar ta yi madallah da wannan jawabi. Sai dai kuma ta yi hakan ne tana mai taka tsantsan a dangane da sharuddan da Netanyahu ya shimfiɗa game da kafa ƙasar Falasɗinu. Ƙasar Finland a ɗaya hannun cewa ta yi wannan jawabi ba zai wadatar wajen inganta dangantaka ba. Shi kuma Shugaban Amirka Barack Obama ya kira amincewar Netanyahu da kafa kasa ta Falasdinu tamkar muhimmin ci gaba. Shugaba Mahmoud Abbas na Falisɗinu ya kira wannan jawabi tamkar ƙafar angulu ga tafarkin samar da zaman lafiya.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita. Mohammad Nasiru Awal