1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin shugabannin ƙasashen duniya game zaɓen Iran.

Abdullahi Tanko BalaJune 14, 2009

Shugabannin duniya sun yi taka tsantsan wajen maida martani game da zaɓen Iran wanda yan adawa ke ƙalubalantar sakamakon da ya baiwa shugaba mai ci Mahmoud Ahmedinejad nasara.

https://p.dw.com/p/I9Kn
Shugaban Iran Mahmoud Ahamdinejad, yayin da yake amsa tambayoyin yan JaridaHoto: AP

Shugabannin duniya sun yi taka tsantsan wajen maida martani game da zaɓen Iran wanda yan adawa ke ƙalubalantar sakamakon da ya baiwa shugaba mai ci Mahmoud Ahmedinejad nasara.

Da farko shugabanin ƙasashen duniyar sun ja bakinsu ne sun tsuke ba tare da cewa uffan ba, suna nazarin alámuran da kan je su komo dake nuni da alamun chanji na sauyin manufa bayan shekaru huɗu na raáyin riƙau da taƙaddamar Nukiliya wanda aka sha fama da shugaba Ahmedinejad mai shekaru 52 da haihuwa. sai dai kuma yan kaɗan daga cikin shugabannin waɗanda suka baiyana martani sun yi hakan ne tare da yin taka tsantsan akan sakamakon wanda yan adawa ke cigaba da jayayya akan sa.

Manyan ƙasashe dai irin su Britaniya da Amirka sun yi kafa-kafa wajen tofa albarkacin bakinsu akan sakamakon da ya baiwa shugaba mai ci Mahmoud Ahmedinejad nasara da kashi 62 cikin ɗari na adadin ƙuriún da aka kaɗa. Abokin hamaiyarsa Hussain Musawi ya sami kashi 32 ne cikin ɗari.

Tuni jagoran addini na ƙasar Ayatollah Ali Khameni ya tabbatar da sakamakon tare da buƙatar ɗaukacin alúmar ƙasar su martaba wannan sakamako.

Ƙungiyar tarayyar turai a martaninta, ta baiyana damuwa game da taƙaddamar da ake kan sakamakon da kuma tarzomar da ta biyo baya.

A nata ɓangaren sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta yi bayani ne da cewa " Mun bi sau da ƙafa shauƙi da kuma muhawarorin da suka gudana yayin wannan zaɓe. Muna cigaba da nazarin alámuran dake faruwa a Iran. To amma kamar sauran ƙasashen duniya mun dakata, mun kuma zuba ido domin ganin shawarar da alúmar Iran suka yanke. Fatanmu shine sakamakon ya dace da haƙiƙanin muradun jamaár Iran ".

Ita kuwa ƙasar Kanada a ta bakin Ministan harkokin wajenta Lawrence Cannon, cewa yayi ƙasarsa ta damu matuƙa game da zargin maguɗi a zaɓen. Yayin da Rasha ta baiyana fatan Ahmedinejad zai nuna sassaucin raáyi a waádin mulkinsa na biyu.

Ƙungiyar ƙasashen larabawa ta hannun sakatarenta Amr Moussa ta aike da saƙon taya murna ga Ahmedinejad, tana mai baiyana fatan Iran da ƙasashen larabawa zasu haɗa hannu wajen tabbatar da zaman lafiya.

Shima shugaban ƙasar Syria Bashar al-Assad ya aike da fatan alheri ga shugaba Ahmedinejad yana mai jaddada fatan dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu zata cigaba da bunƙasa.

Shugaban ƙasar Venezuela Hugo Chavez, ta wayar tarho ya tattauna da Ahmedinejad inda ya taya shi murna ya kuma baiyana masa cewa nasarar da ya samu ta nuna a fili amannar alúmar Iran na wanzuwar sabuwar duniya mai alfahari.

Sauran waɗanda suka aike da saƙwanni sun haɗa da ƙungiyar Hamas wadda ta jinjinawa nasarar Ahmedinejad tana mai cewa nasara ce ta gwagwarmayar kare haƙƙin alúma daga barazanar turawan yamma.

A jawabin da ya yiwa alúmar ƙasar ta akwatunan Talabijin Ahmedinejad ya musanta zargin maguɗi yana mai cewa an gudanar da zaɓen lami lafiya ba tare da wata Almundahana ba.

Sai dai a waje guda yan adawa waɗanda suka ƙi amincewa da sakamakon sun tada bore da zanga-zanga a faɗin ƙasar. Ɗan takarar adawar Hussain Musawi yayi kira ga hukumar zaɓen da ta soke sakamakon. " Daga bayanan da muka samu a dukkan sassan ƙasar nan tabbas ni ne wanda yayi nasara kuma da gagarumin rinjaye".

Duk da ƙalubalantar sakamakon da Musawi yake yi, jamiai da dama da kuma masana na ganin cewa zai fi karkata da miƙa wuya ga ƙasar Amirka. Masu nazarin alámuran yau da kullum a cikin Iran da kuma yammacin duniya sun baiyana cewa sake zaɓar Ahmedinejad zai sosawa yammacin turai waɗanda ke hanƙoron dakatar da shirin Nukiliyar Iran.