1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Jamus akan rahotan Baker

December 7, 2006
https://p.dw.com/p/BtxA
Frank Walter Steimeier
Frank Walter SteimeierHoto: AP

Yan siyasa dake nan jamus sunyi maraba da shawarwarin da komtin da James Baker kewa jagoranci ya gabatar wa shugaban Amurka jiya adangane da bukatar sake nazarin halin da zaa ceto Iraki,tare da bin hanyoyin diplomasiyya da makwabtan da suka hadar da Iran da Syria wajen gano bakin zaren warware rikicin da kasar ke cigaba da kasancewwa ciki.

Kafin barinsa birnin Berlin yau zuwa Amurka,inda zai gudanar da ziyarar kwanaki biyu,ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier,ya fadawa Dw cewa zai tattauna da takwararsa ta amurka Condoleeza rice,adangane da halin rashin tsaro da Iraki take ciki..............

Yace kasashen turai da Amurka zasu taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya baki daya.

A wannan ziyara tasa ta kwanaki biyu a birnin washinton,Steinmeire zai gana da yan majalisar dottijai daga jammiiyun Republikan da takwarorinsu na Democrat.Wannan ziyara tasa nada nufin yada manufofin ketare na jamus,makonni hudu gabannin karban kujerar shugabancin kungiyar tarayyar turai Eu.

Manazarci kann harkokin ketare daga jammiyar FDP anan jamus Wolfgang Gehard,ya yabawa rahotan na komitin Baker, da kuma shawarwari da suka bayar adangane da ainihin halin da kasar take ciki.

Shima Jürgen Trittin na jammiyar The Greens,yana mai raayin cewa warware rikicin kasar iraki zai iya samun nasara ne kawai da taimakon kasashen Iran da Syria.

Kakakin bangaren yan majalisar dokokin jammiyar CDU Eckart Von Klaeden yace,abu mafi mihimmanci dangane da rahotan komitin na Baker ,shine halin da Iraki ke ciki nada nasaba da manufofin Amurka a wannan kasa.Inda yayi karin bayani dacewa.....

"Iraki tana cikin hali mawuyaci na tashe tashen hankula,cigaba da kasancewar dakarun Amurka a wannan kasa,zai dada zubar da martabar hanyoyin da zaa bi na samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya baki daya."

Jamus dai tana da rawa da zata taka cikin harkokin samar da zaman lafiya a Iraki,ta hanyar bada ilimin horarwa wa jamian tsaro na kasar.

Berlin dai na da nufin amfani da kujerar shugabancin TT dana kungiyar G 8 masu cigaban masanaantu da zata karbi,ragamarsu a watan janairu,wajen farfado da daftarin samarda zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.