1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin kasashe kan manufofin Amurka a Iraki

Zainab A MohammedJanuary 11, 2007

Magabatan Iraki sunyi maraba da manufofin da Amurka ta gabatar,dacewa zasu bada hadinkansu

https://p.dw.com/p/Bu4v
Premiern Iraki Nuri al Maliki
Premiern Iraki Nuri al MalikiHoto: picture-alliance/dpa

Washinton ta gano dakarun Mehdi, wadanda ke marawa fitaccen limamin yan shian nan Moqtada al-Sadr baya, amatsayin wadanda ke barazana wa harkokin tsaro a kasar ta Iraki,amma kuma gwamnatin prime minista Nuri Al Maliki na dogoro da goyon bayansu acikin harkokin gudanarwa.

Masu lura da lamura dakaje suzo dai sun soki lamirin gwamnatin maliki na gaza tabuka komai watanni takwas bayan hawanta mulki adangane da halin da yan irakin ke cigaba da kasancewa a ciki na rashin tsaro.A kullum dai darurun mutane ne ke mutuwa sakamakon hare haren sojojin sakai da boma bomai,da wasu makamai makamantansu,da kisan kabilanci.

A taron manema labaru da ya gudanar a washinton,sakataren tsaron Amurka Robert Gates yayi karin haske dangane da irin rawa da dakarun Amurkan zasu taka a wannan kasa dacewa.

Yace wannan tsarin ya kunshi cewa dakarun Irakin ne zasu jagoranci wannan kamfaign na tabbatar da tsaro,ayayinda dakarunmu zasu mara musu baya ne kadai,domin kare rayukan alummomin bagadaza daga hare haren masu fadan kiyayya,tare da bawa gawamnatin Irakim daman shirya yadda zata rataya alhakin tabbatar da kare jamaarta.

To sai dai Robert Gates ya bayyana cewa har yanzu babu sahihin waadin kasancewar dakarun Amurkan da shugaba Bush ya sanar, akasr ta Iraki.

Shima daya ke mayar da martani dangane da wannan mataki da Amurkan ta dauka mukaddashin shugaban jammiyyar SPD a majalisar dokokin jamus,Walter Kolbow cewa yayi.

Agaskiya kara adadin dakarun bashi ne zai iya magance ayyukan yan ta kife akasar Iraki ba.

A nata bangaren sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta bayyana cewa tuni yan Irakin da kansu suka dauki matakai da suka hadar da yadda zasu tafiyar da harkokin siyasan su da tattali da tsaro,kuma kokarin Amurka shine ta bawa gwamnatin goyon baya.

To sai dai tuni Britania ta bayyana goyonb bayanta da wadannan sabbin manufofi na Amurka a kasar ta Iraki,sai dai tace bazata bada karin sojojinta zuwa wannan kasa ba.Kamar yadda sakatariyar harkokin waje Magret Beckett ta bayyana.”Ayanzu muna tunkarar halin da ake ciki a Basra ,ba raayimmu bane a wannan lokaci mu tura karin dakarun soji zuwa Iraki,Muna fatan cigaba da kokarin daidaita lamura a Basra da kuma mika ragama ga jamian tsaron na Iraki”.

Shi kuwa shugaban komitin kula sda harkokin ketare a majalisar dottijai na A,urka sen Joseph Biden ,cewa yayi wadannan manufofin na Bush mummunan kuskure ne ,domin wannan ba shine hanyoyin da zaa bi na warware rikicin kasar ta Iraki ba.