1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin kasashe kan sakamakon zaben Turkiyya

July 23, 2007

Jamiiyya AK ta Premier Erdogan ta lashe zabe

https://p.dw.com/p/Btuz
Premier Tayyip Erdogan na Turkiyya
Premier Tayyip Erdogan na TurkiyyaHoto: AP

Kungiyar tarayyar turai EU ta yabawa sakamakon zaben kasar Turkiyya inda jamiiyyar prime minister Tayyip Erdogan dake da tushen addinin Islama ta AK ta sake samun zarcewa ,tare da kira a gareta data matsanta batun gyare gyare a harkokin mulki domin bata daman shiga kungiyar.

Nasaran da jamiiyyar masu raayin mazan jiya ta Ak ta samu a turkiyyan dai na mai kasancewa,zai dada karfafa mata kwarin gwiwa adangane da shiganta kungiyar ta Eu,wadda aka fara a shekara ta 2005,sai dai har yanzu shugaba Nicholas Sarkozy na kasar faransa na adawa da shigar da Ankara wannan kungiya ta EU.

Shugaban hukumar gudanarwa na kungiyar EU,Jose Manuel Barroso,ya mika sakon taya murnarsa wa Erdogan tare da sake laakari da kokarinsa na hadewa a kungiyar.

Shima dan majalisar turai daga jammiiyyar The Greens na nan jamus Cem Özdemir, cewa wannan wata damace wa Erdogan na yiwa harkokin gwamnatinsa garon bawul,wanda hakan ne sharan fagen amincewa da ita a kungiyar ta Eu.

Oton

Shima dan siyasa daga jammiiyyar CDU mai raayin yan mazan jiya dake nan jamus Eckert Von Klaeden,fata yayi nacewa sakamakon wannan zaben dama abune da aka rigaya aka hanga…

“Yace daman an rigaya an yi hasashjen sakamakon zaben,don haka ba wani abun mamaki bane.Sai dai abunda keda muhimmanci anan shine kasancewa jammiiyyar ta AK mai tushen addini,ta cigaba da tabbatar manufofin da ta sanya a gaba”.

Jaridun kasar Girka ayau dai sunbayyana wannan sakamakon zaben na turkiyya sukayi da kasancewa wata koma baya wa rundunar sojin kasar,da zasu kawo sauyi tsakanin yankuna dake adawa da juna.

Wasu jaridun kuwa cewa sukayi prime minister Erdorgan zai iya fuskantar gagarumin adawa daga rundunar dama sauran jamiiyyun adawa dake wannan kasa.

Ita kuwa fadar paparoma ,bayyana sakamakon wannan zabe tayi da kasancewa mafi ingancin irinsa a nahiyar turai da kuma wa majamiun almasihu baki daya.Daya daga cikin limaman fadar paparoman Cardinal Sergio Sebastiani a hiran da jaridun birnin Rome sukayi dashi,yayi kira ga kunguiyar tarayyar turai Eu data koma tattauna shigar Turkin kungiyar.

Kakakin kungiyar Hamas dake da madafan Iko a yankin Gaza Sami Abu Zuhri,a sakon taya murna amadadin kungiyar yace nasarar jammiiyyar ta Ak ,na dada bayyana cewa dole ne musulmi su dogara da addini a matsayin makoma nan gaba.