1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin kasashen dunia a game da kalamomin shugaban kasar Iran

Yahouza sadissouOctober 27, 2005

Kasashen dunia na bayyana ra´ayoyi a kan kalamomin shugaban kasar Iran

https://p.dw.com/p/Bu4a
Iran
IranHoto: dpa

Mataimakin Praministan Israela Shimon Perez, ya maida martani, ga kalamomin shugaban kasar Iran Mahamud Ahmadi Nejad.

Jiya ne shugaban na Iran, ya gabatar da wani jawabi a taron lacca gaban dalliban kasar, su fiye da dubu 3, inda ya kada baki ya ce, kwata-kwata kamata tayi, a shafe haramtaciyar kasar Israela daga doran kasa.

Bai dace ba,sam inii shi, kasashen larabawa, su amince bani yahudu, tsofin abukan gabar su,su girka kasa, a tsakiyar yankin larabawa.

Mataimakin Praministan Israela, ya rubuta wasika zuwa ga Ariel Sharon , inda ya bukaci cikin gaggawa Israela ta aika bukatar ta ga sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan, da komitin Sulhu, domin a kori Iran, daga sahun kasashe membobin Majalisar Dinkin Dunia.

A cewar Shimon Perez ba ta kamata, a daidai lokacin da a ke neman zamen lahia mai dorewa a dunia, bai dace ba, a daidai wannan lokaci, da ka shiga tantanawa ta zahiri, tsakanin Isrela da Palestinawa, tare da sa hannun kasashe da kungiyoyi na dunia, wani shugaban kasa, ya fito ya na wannan kalamomi na batanci da renin wayo.

Mataimakin Praministan ya kara da cewa, wannan huruci na tabbatar wa dunia, karakara ,shugaban kasar na Iran, dan ta´ada ne, kamar yada da dama su ka ambata, jim kadan bayan zaben sa, kuma hakan wani karin shaida ne, na cewar ba banza, Iran ke fadi ka tashi tashin kira makaman Nuklea.

Babar manufar da su ke bukatar cimma ko shaka babu, itace ta kaiwa Israela harin kare dangi.

Kamin wasikar ta mataimakin praminista, shima ministan harakokin wajen Israela, Sylvan Shalom ya nuni Iran da kasa mai cike da hadar,i da kuma mumunar aniyar hallaka Israela da israelawa, da zaran ta samu sarari, a dalili da hakan ne, Sylvan Shalom ya gayyaci kasashen dunia, da su gaggawta daukar matakin gurfanar da ita gaban komitin sulhu na Majalisar Dunia, a game da shirin ta, na kera makamman Nuklea..

Ya zuwa yanzu,Kasashe daban daban na dunia sun fara bayyana ra´ayoyi a game da hurucin na shugaban kasar Iran.

Kasar Fransa itace kasar farko, da ta fara kiran jikadan kasar Iran a Paris, inda ta bayyana masa rashin jin dadi, a game da wanan jawabi wanda kan iya tada zaune tsaye a cikin dunia.

A cen birnin Washington, kakakin fadar White Hause, ya ce Amurika, ta damu matuka da wannan bayyani, na Ahmadu Nidjad, wanda ke tabbatar da tuhumar da Amurikawa ke yi wa Iran da mallakar makaman kare dangi.

A nan ma kasar Jamus, hukumomi sun bayyana takaici , a game da huruncin na shugaban Iran.

Tun bayan shekaru da dama da su ka wuce, wannan shine karo na farko, da wani shugaban kasar ke fitowa hili, ya kalubalanci Israela, ta hanyar a shafe ta baki daya, daga jerin kasashen dunia.

Saidai, ba abu ne na boye ba, cewar shuwagabanin kasashe daban daban na Iran, ba su amince ba, gaba daya da Israela.

To amma duk da haka, Shugaban kasar da ya gabata, Muhamed Khatami a tsawon mulkin sa, ya nuna sassauci ga tofin Alllah tsine da Iran ke yi wa bani yahudu.

Ahmadu Nidjad, wanda tsofan member ne,a komitin zartaswa na juyin juwa hali, bisa jagorancin Imam Komeini,da ya hau mulki a watan Ogust, da ya wuce, ya ce babu gudu babu ja da baya, a game da adawa tsakanin Iran da Isra´ila.