1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Nijar akan hukuncin kotun ECOWAS

November 11, 2010

Hukumomin Nijar sun sanar da cewa ba zasu saki tsohon shugaban ƙasar ba Tanja Mamadu ba

https://p.dw.com/p/Q6TA
Shugaban gwamnatin mulkin Nijar Janar Salou Djibo da wasu wakilai na ƙetare a YamaiHoto: AP

Gwamnatin Janhuriyar Nijar ta mayar da martanni dangane da hukuncin da kotun ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta yanke a farkon wannan mako kan cewa tsaron da sojojin suke yi wa tsohon shugaban ƙasar Tanja Mamadu ya saɓama doka.

Ana tsare da Tanja ne da tsohon ministansa na cikin gida Abuba Albade tun a cikin watan Fabrairu da ya gabata bayan juyin mulkin da sojojin suka yi masa.

A wani taron manema labarai da ya kira kakakin gwamnatin Dokta Lawali Mahaman Ɗanɗa ya shaida cewa suna da ja akan wannan hukunci domin kuwa ya ce za su bi duk hanyoyin da suka dace na ganin sun ɗaukaka ƙara akan wannan hukunci domin soke shi saboda ya ce tsaron da ake yi wa tsohon shugaban ana yin sa ne don kare lafiyarsa.

Shi dai tsohon shugaba Tanja ya sha suka bayan da ya canza kundin tsarin mulkin ƙasa domin ya samu damar yin tazarce. Su sabbin hukumomin ƙasar a kwanakin baya sun shirya zaɓen raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki na janhuriya ta bakwai, wanda sakamako ya nuna al'umma ta amince da shi.

Mawallafi: Abdurahamane Hassane

Edita: Mohammad Nasiru Awal