1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MARTANIN SHUGABANNIN KASASHEN DUNIYA KAN RASUWAN ARAFAT DA SAKONNIN TAAZIYYARSU.

November 11, 2004
https://p.dw.com/p/Bvei
Marigayi Shugaba Yasser Arafat na Palasdinu da Shugaba Gehard Schroder na Jamus.
Marigayi Shugaba Yasser Arafat na Palasdinu da Shugaba Gehard Schroder na Jamus.Hoto: AP

Shugabanin duniya sun bayyana Mutuwar kwarzon namiji kuma shuagban palasdinawa a matsayin bababn rashi ba wai wa alummar palasdinawa kadai ba,koda yake raayi ya banabanta dangane da irin gudummowa daya bayar wajen samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsaki.

Duk da sabanin raayi da aka samu tsakanin shugabanni kann ire iren rawa da Arafat ya taka wajen zaman lafiyan yankin gabas ta tsakiya,sun hade wajen kira da kawo karshen zubar da jini da aka dauki shekaru da dama anayi a wannan yankin,tsakanin palasdinawa da Israela,tare da bukatar bawa Palasdinawan yancin cin gashin kansu.

Prime minista Ariel Sharon ya bayyana mutuwan Mallam Arafat abokin fafatawarsa da kasancewa wani juyi a tarihin yankin gabas ta tsakiya,ayayinda shugaba George W Bush na Amurka ya bayya rasuwansa da kasancewa muhimmin batu a tarihin Palasdinawa.

Sharon yayi fatan cewa sabbin shugabannin Palasdinun zasuyi laakari da inganta dangantakarsu da Osraela,ta hanyar kawo karshen ayyukan tarzoma dake wannan yankin.Shi kuwa Bush wanda yayi kokarin tauye Arafat lokacin daya haye gwamnati a shekara ta 2001,yayi fatan Palasdinawa zasu zauna lafiya da makwabtansu ,wanda shine zai kasance hanyar samun yancin cin gashin kai da suka jima suna gwagwarmayan nema.Bush wanda ya kasance shugaban Amurka na farko daya amince da shirin mikawa palasdinawa yancin kai,yasha sukan lamirin marigayi Arafat.

Shi kuwa sakatare general na mdd Kofi Annan bayyana marigayin yayi, da kasancewa gwarzon shugaba daya cikanta burin jamaarsa tare da hade kawunanasu wuri guda.Yace bayan rattaba hannu kann yarjejeniyar birnin Oslo a shekara ta 1993,yayi namijin kokari wajen tabbatar da cimma burinsa,sai kuma gashi rai yayi hali.

Shugaban Israela Moshe Katsav,ya bayyana rasuwan Arafat da kasancewa sabon babi a harkokin siyasan yankin.

A nasu bangare yan siyasan kasashen turai dake marawa Arafat baya a matsayin zabbaben shugaban yankin Palasdinu,cewa sukayi rasuwarsa zai bawa bangarorin biyu damar komawa teburin sulhu domin warware rikicin dake tsakaninsu.Jamiin harkokin waje na kungiyar gamayyar Turai Javier Solana yace ,abu guda daya rage na tunawa da shaugaban Palasdinawan shine tabbatar zaman lafiya a yankin tare da tabbatar yantacciyar kasar Palasdinu.

Tony Blair na Britania yace,yanzu damuwan alumman duniya itace zaman lafiya tsakanin Israela da Palasdinu,inda yace zasu Amurka da kungiyar EU zasu taka rawa wajen daidaita bangarorin biyu.

Shugaban Faransa Jack Chirac wanda ya ziyarci asibitin da Arafat yayi jinya zuwa rasuwarsa yau da safiya,ya mikawa mai dakinsa ,da sauran iyalinsa ,yanuwa da abokan arziki da alummar Palasdinu gaisuwan taaziyarsa.Chirac ya bayyana Marigayin da kasancewa gwarzon namiji wanda har ya cika,yana nemarwa alummarsa hakkinsu.Ayayinda ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer,ya bayyana rasuwan Arafat da kasancewa babban rashi dazai zamanto tarihi wa Alummar Palasdinu.

Tsohon Shugaban amurka Bill Clinton ya aike da nashi sakon taaziyya.

Shi kuwa Shugaba Vladimir Putin na Rasha,bayyana Arafat yayi da kasancewa gwarzon shugaba na siyasa daya dauki hankalin duniya,mutumin yayi gama rayuwarsa wajen nemarwa alummarsa hakkinsu.Itama kasat Tunisia data marabci tare da daukan nauyin headquatan kungiyar neman yancin Palasdinawa daga shekara ta 1982-1994,ta bayyana Arafat da kasancewa gwarzo kuma wayayyen shugaba,acikin sakon taaziyya da shugaba Ben Ali ya aike da ita.

Sauran shugabanni da suka aike da sakonnin taaziyyarsu sun hadar da Shugaban Indonesia Susilo Bambang,da shugaban kungiyar kasashen musulmi prime minista Abdullah Ahmad Badawi,da Paparoma John Poul na biyu da kuma shugaba Hu Jintao na kasar Sin,wadanda ke yabawa irin kokarin marigayin wa yankinsa.

Shi kuwa Sarki Abdulla na Jordan ya sanar da kwanaki 40 na makokin a masarautar kasar,kana yini uku na kasa baki,domin girmama wannan gwarzon namiji tsakanin alummar larabawa.