1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin soke zaben Kenya

Usman Shehu Usman
September 1, 2017

Kotun kolin kasar kenya ta soke zaben shugaban kasar da aka yi a watan jiya kotun wace ta saurari korofin 'yan adawa ta yi bayanai da suka kai ga soke zaben wadanda suka hada da kurarai daga hukumar zabe.

https://p.dw.com/p/2jE3i
Bildkombo Kandidaten Wahlen Kenia 2017

Jagoran 'yan adawan kasar ta Kenya Raila Odinga, ya bayyana hukuncin da aka yi a matsayin wani ci gaban demokradiyar Afirka baki daya.

"Wannan babban tairihi ne ga al'ummar Kenya dama a fadin Afirka baki daya. A karon farko cikin tarihin demokradiyar Afirka, an samu hukuncin da ya soke zabe  bisa kura-kurai da aka tabka a zaben shugaban kasa"

Tun da farko dai hukumar zaben kasar Kenya ta ayyana Shugaba Uhuru Kenyatta, a matsayin wanda ya lashe zabe da ya gudanan ranar 08.08.2017, amma yan adawa suka ce da sakel. A lokacin kungiyoyin sa'ido kan zabe daga kasashen duniya, duk sun yaba da zaben kuma suka kwatanta shi a matsayin mai tsabta wanda aka yi bisa ka'ida.

Shugaba Kenyatta a martaninsa ya sanar da yin watsi da soke zaben da kotu ta yi, amma ya ce zai yi biyya ga hukunci don haka zai sake komawa fagen daga don neman jama'a.

Yanzu dai kotun kolin na kasar Kenya ya bada umarnin a gudanar da sabon zabe nan da kwanaki 60.