1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar da makwabtanta Beirut da Gaza dake fama da rikici

Zainab A MohammedDecember 21, 2006
https://p.dw.com/p/Btwv
Shugaba Hosni Mubarak na Masar
Shugaba Hosni Mubarak na MasarHoto: AP

Ayayinda Iraki da Amurka tayi kakagida,ke cigaba da kasancewa cikin halin rigin gimu na kabilanci da addini,Masar ta mayar da hankali kann makwabtanta guda biyu dake fama da rikicin siyasa,watau Yankin palasdinawa da Lebanon,wadanda ke bakin fadawa yakin basasa.

Duk dacewa matsaloli da ringimun siyasa a yankin zirin gaza da birnin Beirut sun jagoranci daukan matakai na diplomasiyya a bangaren Alkhahira,har yanzu babu alamun zaa cimma wani tudun dafawa,a kokarin warwaresu.

Kokarin kafa gwamnatin hadin kann kasa a yankin palasdinawa tsakanin jammiyar adawa ta fatah da ta hamas mai mulki,ya gaza,sakamakon rashin cimma daidaito akan rarraba madafan iko.Adaura da haka kuma kiran da shugaba mahmooud Abbas yayi dangane da gudanar da sabon zabe na yan majalisa cikin gaggawa a karshen makon daya gabata,ya dada haifar da sabbin tashe tashen hankula tsakanin bangarorin biyu,musamman a bangaren hamas wadda keda rinjaye a majalisar dokokin yankin.

A martaninsa daya mayar,premier Ismail Haniya ya bayyana kiran na shugaba Abbas da kasancewa wani yunkuri ne daya sabawa kundun tsarin mulkin yankin.

Ya dai zargi wannan yunkuri da kasancewa wata damace na kifar da gwamnatinsa,wadda yace da sa hannun Amurka a ciki.A inda anan take fada ya barke tsanin bangarorin biyu,wanda yayi sanadiyyar mutuwan mutane 6 a zirin gaza ,duk da kiran da akayi na tsagaita wuta.

A kokarin data sabayi na shiga tsakani wajen warware rigingimu na cikin gida a yankin na palasdinawa,masar tayi fatan cewa zaa cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin bangarorin biyu .

Mataimakin directa dake cibiyar nazarin dabarun siyasa a al-Ahram dake birnin Alkhahira Mohammed Sayyed,yace masar din ta duka kain da nain wajen warware wannan rikici,ta hanyar jaddada bukatar kafa gwamnatin hadin kann kasa.

Kazalika ,bayan jan hankalin kungiyar fatah,masar zata kuma yi kokarin ganin cewa ta tuntubi hamas,kungiyarda aka kafa akan tafarkin kokarin neman yancin yan tacciyar kasa daga mamayen izaela,data sassauta kallon da takewa izraelan.To sai ya zuwa yanzu kungiyar ta hamas wadda keda cibiyarta a birnin Damascus,taki laakari da izraelan a matsayin yantacciyar kasa.

Masar din dai a kokarinta na farfado da sulhunta izraela da palasdinawa,ta kirkiro batun musayar prisononi.Rahotannin kafofin yada labarin masar din na nuni dacewa,kasar ce ke kokarin ganin cewa an sako daruruwan palasdinawa dake kurkukun izaraelan ,amadadin kofur na sojin izraelan da da mayakan sakai na palasdinun suka cafke tun daga watan yuni ,wanda ya janyo somame da dakarun izraelan sukayi a zirin gaza,wanda ya kashe palasdinawan 500 kafin a cimma tsagaita wuta a watan Nuwamba.