1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mashigin ruwan Bermuda Triangle

August 20, 2010

Jiragen sama da na ruwa da dama ne suka ɓace, kana wasu mutane masu yawan gaske suka halaka a wannan yanki

https://p.dw.com/p/OsPT
Hoto: AP

Shekaru da dama kenan dai ake bada labarin wannan mashigi ko tsibiri na Bermuda Triangle kamar yadda aka san shi. Labaran da kuma yake tattare da ban al'ajabi da kuma bantsoro. Shidai wannan mashigi yayi kan iyaka ne da yankin ruwan Florida na Amirka da tsibirin Bahamas da kuma Karebiyan, sai kuma tekun Atilantika ta gabas har kuma ya haɗe da gaɓar ruwan Miami da kuma Puerto Rico. Akasarin hatsuran dake da nasaba da wannan mashigi na Bermuda dai suna aukuwane a waɗannan yankuna.

Mashigin ruwan yankin na Bermuda dai ya kasance wani yanki ne da ake samun zirga-zirgan jiragen ruwa na kasuwanci da na 'yan yawan buɗe da kuma jiragen sama. kuma bisa la'akari da hatsarun da akayi ta samu dake da alaƙa da ɓacewar jiragen ruwa, ko na sama yasa marubuta da masu sharhi da sauran masu bincike suka duƙufa wajen wallafa ƙasidai da dama game da gaskiyan abinda a ganin su yake haifar da wannan abin al'ajabi.

Wata ƙasida da George X. Sand ya wallafa a shekarar 1962 tayi bayani game da ɓacewar wasu jiragen saman yaƙin Amirka guda biyar, a lokacin wani atisayen soji a watan Decenban 1945. Bayanan da aka samu na ɗaya daga cikin direbobin jirgin saman yaƙin a wancan lokaci dai yace, suna shiga wani ruwa mai alaman kore, a maimakon farin ruwa, kafin a daina jin ɗuriyar sa.

To wani abinda mamaki kuma sheni yadda wani katafaren jirgin ruwan sojin Amirka mai ɗauke da sojoji 35 da aka tura domin gano wa'yannan jiragen saman biyar shima ya ɓace sama ko ƙasa.

Tarihi dai ya nuna cewar akwai jiragen sama dana ruwa a ƙalla goma sha huɗu da ɗaruruwan mutane da suka ɓace a tsakanin wannan tsibiri da mashigin na Bermuda Triangle.

Wasu masanan kimiya dai na danganta hatsuran ne da ƙarfin igiyar ruwan teku tare da iska mai ƙarfi da ake fuskanta a wannan yanki. A yayin da wasu kuma ke ganin lamarin na da alaƙa ne da wasu ƙwama-ƙwamai ko Aljanu ko kuma Iska. Har yanzu dai malaman kimiya naci gaba da bincike game da wannan mashigi na Bermuda Triangle ba tare da gano dalilan wayanan hatsura ba.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Zainab Mohammed Abubakar