1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masifar wutar daji da zafin rana da kuma ambaliyar ruwa a Turai

July 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuFF

Wutar daji na ci-gaba da addabar yankuna da dama a kudanci da kudu maso gabashin Turai wadanda ke fuskantar masifar zafin rana a cikin makonnin nan. Kasar Girika ta fi fuskantar wannan matsala, kuma yanzu haka jami´an kwana kwana ke aiki ba dare ba rana don kashe wutar daji a yankuna daban daban na kasar. A kuma kudancin Italiya har yanzu ana aiki da wata dokar ta baci sakamakon zafin ranar da ake fama da shi. A kuma halin da ake ciki an yi hasashen cewa Ingila da Wales zasu samu karin ruwa sama mai yawa a karshen wannan mako. Hakan ya zo a ne a daidai lokacin da ambaliyar ruwa a wasu sassa na Ingila ta fara raguwa. Jami´ai sun ce har yanzu wasu gidaje kimanin dubu 100 a yankin Gloucestershire ba su da ruwan famfo.