1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu aikin agaji na gamuwa da cikas a ƙasar China

August 12, 2010

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka sake sheƙawa a ƙasar China ya dagula lamarin masu aikin ceto

https://p.dw.com/p/OmYJ
Hoto: AP

 Ayyuka agaji na ceto jama'a da zaɓtarwa ƙasa ta rutsa da su a ƙasar China sakamakon ambaliya ruwan   da aka samu na gamuwa da cikas dangane da wani ƙarin ruwan samar kamar da bakin ƙwarya da aka sheƙa a daran jiya larba.

Mutane dai sama da dubu guda ne suka mutu a yankin arewa maso yammacin ƙasar yayin da 1700 suka yi ɓatan dabo a sanadiyar zaɓtarewar ƙasa da aka samu dakuma zubar laka a wasu yankunan dake kan tsauni.

kamfanin dilacin  labarai na ƙasar Faransa AFP, ya ambato wani  mai aikin agajin  Han Huiping na ƙasar ta China  ya na mai cewa kusan awowi fudu da aka ƙwashe a jiya ana tabka ruwan saman 

ya sa hanyoyin sun sake datsewa, abinda kuma ya ce ya kawomasu cikas ga aikin rabon ruwan sha  na pompi da kuma cimaka da suke yi ga jama'a

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita       : Zainab Mohammed abubakar