1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu binciken kisan Hariri sun yi wa shugaban Lebanon Lahoud tambayoyi

November 12, 2005
https://p.dw.com/p/BvLU

Wata tawagar MDD dake binciken kisan gillar da aka yi wa tsohon FM Lebanon Rafik Hariri ta yiwa shugaban Lebanon mai goyon bayan Syria Emile Lahoud tambayoyi. Wata sanarwa da ofishin shugaban ya bayar ta ce shugaba Lahoud ya gana da jami´ai biyu na wannan tawaga ta kasa da kasa a jiya da yamma kuma ya yi musu bayani dalla-dalla ba da wata rufa-rufa ba dangane da wata hirar ta wayar tarfo da ofishin sa yayi gabanin kai harin wanda ya halaka Hariri da wasu mutane 20 a cikin watan fabrairu. Wannan dai shi ne karon farko da shugaba Lahoud ya gana da tawagar binciken ta MDD a karkashin jagorancin mai daukaka kara na Jamus Detlev Mehlis. Ko da yake rahoton MDD bai shafawa Lahoud kashin kaji ba, amma binciken ya nuna cewa wani da ake zargi da hannu ya bugawa shugaban waya kafin fashewar bam din.