1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu jajayen riguna sun yi biris da cikan wa'adi

May 17, 2010

Madugun 'yan adawan Thailand ya mutu a raunin da ya samu na harbi

https://p.dw.com/p/NQ8i
Hoto: AP

A ƙasar Thailand an tabbatar da mutuwar shugaban 'yan adawa Manjo Janar Khattiya Sawasdipo. Janar ɗin wanda ya canza sheƙa ya koma ɓangaren 'yan jajayen riguna dake zanga-zanga ya rasu ne a wani asibitin birnin Bangkok sakamakon mummunan raunin da ya samu a ka biyo bayan harbin da aka yi masa a ranar Alhamis da ta gabata. A mummunar arangama da ake tsakanin jami'an tsaro da 'yan adawa an kashe fararen hula 37 sannan sama da 300 suka samu raunuka a cikin kwanaki huɗu. Duk da cikar wa'adin da gwamnatin ta bayar har yanzu masu zanga-zangar kimanin 5000 na ci-gaba da mamaye cibiyar hada-hadar kasuwanci ta birnin Bangkok. Da farko dai masu jajayen rigunan sun yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta shiga tsakanin domin sulhu, amma gwamnati ta ce sai masu zanga-zangar sun yi saranda tukuna.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala