1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu rajin kare muhalli 200 ne aka kashe a 2016

Salissou Boukari
July 13, 2017

Wani rahoto da kungiyar Global Witness mai rajin kare muhalli ta fitar a wannan Alhamis din, ya ce akalla mutane 200 masu fafutikar kare muhalli aka kashe a shekara ta 2016 a duniya

https://p.dw.com/p/2gV7N
Ermordung Ashaninka Stamm  Führer Tochter
Diana Rios Rengifo 'yar wani babban dan gorgomayawa kan muhalli na kasar Honduras.Hoto: Getty Images/AFP/J. Samad

Rahoton ya zayyana sunayen kasashe inda lamarin yafi kamari. A kasar Brazil an kashe mutun 49, a Kolumbiya 37, a Philippines mutun 28, a kasar Indiya mutane 16 inda kungiyar mai zaman kanta ta ce su ne kasashen da aka fi samun kashe-kashen mutanen da ke fafutikar kariyar muhalli, adadin da kungiyar ta ce ya yi munin gaske, inda a shekara ta 2015 aka kashe mutane 185 masu fafutikar kare muhallin a duniya a wurare kamar na hakar mu'adinai, gandun daji, ko kuma cikin ruwa.

Masu fafutikar kariyar Muhalli dai a duniya na kara karuwa, sai dai kuma masu neman gurbata muhalli da ke adawa da hakan na yi musu daukan dauki dai-dai a fadin duniya, inda kungiyar ta Global Witness ta ce kashi 40 cikin 100 na mutanen an kashe su ne a yankunansu.