1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu Zanga-Zanga sun buƙaci sauke Shugaban Hukumar Zaɓen Najeriya

March 31, 2010

Ƙungiyar ƙwadagon Najeriya tayi kira ga Muƙaddashin Shugaban Najeriya da kada ya sake naɗa shugaban Hukumar Zaɓen ƙasar Mourice Iwu

https://p.dw.com/p/MjaH
Muƙaddashin Shugaban Najeriya Jonathan Goodluck.Hoto: AP

Ƙungiyar ƙwadagon Najeriya tayi kira ga Muƙaddashin Shugaban Najeriya Jonathan Goodluck da kada yakuskura ya sake naɗa shugaban Hukmar Zaɓen  ƙasar Mourice Iwu a matsayin shugabar Hukumar.

A wata zanga-zangar lumana da suka gudanar a Abuja, shuganin ƙungiyar ƙwadagon sun shedawa 'yan majalisar dokokin cewar, zasu shiga wani yajin aiki na sai baba ta gani muddin suka bari aka sake naɗa Mourice Iwu a matsayin shugaban hukumar karo na biyu.

Shi dai Mourice Iwu an zarge shi ne da kasa gudanar da amintaccen zaɓen ƙasa a shekara ta 2007, zaɓen da masu saka ido na ciki da wajen ƙasar sukace an tafka gagarumin maguɗi.

Sai dai Mourice Iwu ya ɗora laifin ne akan 'yan siyasa dake ɗaukan batun zaɓe na ko'a mutu, ko ayi rai. A watan juni ne dai, wa'adin farko na shekaru biyar na Mourice Iwu ke cika.

Yanzu haka dai majalisun dokokin ƙasar biyu sun duƙufa wajen yin gyara a kundin tsarin mulkin ƙasar kafin zaɓen shugaban ƙasa da za'a gudanar a shekara mai zuwa.          

Mawallafi: Babangida Jibril, Edita: Zainab Mohammed Abubakar