1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata a harkokin siyasar Turkiyya

July 26, 2007

Mata sun taka rawar gani a zaben majalisar daya gudana a Turkiyya....

https://p.dw.com/p/Btuv
Mace na kada kuria
Mace na kada kuriaHoto: AP

A karon farko mata sun samu kashi 8.7 daga cikin 100 na yawan kujeru dake majalisar dokokin kasar Turkiyya.Wannan dai babban cigaba ne a bangaren matan kasar,wanda ya taallaka akan kokarin da mata malamai keyi na wayer dakai.

Tun daga shekarata 1934 nedai,matan turkiyya suka samu yancin shiga harkokin zabe,shekaru 73 kenan a karon farko an samu wakilai 48 a majalisar dokokin kasar bayan zaben daya gudana a ranar lahadi.

Turkiyyan dai kasa ce dake da raayin ganin cewa an cike gibin da ake dashi ta bangaren mata wajen basu damar tafiyar da harkokin kasa.A dangane da hakane a jamioi da harkoki na yancin dan adam da harkoki gudanarwa na kudi ,matan ne suka mamaye wadannan wurare.

A karkashin sabon tsarinta na gyare gyaren datake gudanarwa cikin harkokin tafiyar da mulkin kasa,akwai bukatar kara bawa matan damar fada aji cikin harkokin gwamnati da sauran bangarori.

Daya daga cikin cibiyoyi dake taka rawar gani a wannan bangare kuwa itace wata cibiyar faftukar nemarwa mata yanci a harkokin siyasa da ake kira Kürzel Kader a takaice.Cikin watannin gabannin zaben Turkiyyan dai cibiyar ta KADER ta gudanar da kamfaign ta gidajen talabijin mai hoto da Radio da manne mannen hotuna dake dasa ayar tanbaya,kan matsayin mata a majalisar gudanarwar kasar.

Hülya Gülbahar dai itace shugabar wannan cibiya…

“sakamakon karshe dai ya nunar dacewa,bamuyi kanpaign a banza ba.Munyi matukar aiki,kuma sakamakonsa shine ninka yawan mata wakilai da ake dasu a majalisar dokoki.a karo na farko mun shaidar dacewa majalisar Turkiyya nada mata wakilai masu yawan gaske.Wannan itace Turkiyya,kuma wannan shine Demokradiyya a Turkiyya ,mai kyakkyawan sakamako.A kasar turkiyya dai akwai yancin mata…”

Suma mata dake koyarwa a jamioin kasar dai sun bada tasu gudummowa a cikin harkokin siyasar Turkiyyan,wajen taimakawa mata yan uwansu.

Professor Türkel Minibis dake jamiar Istambul tayi karin haske dacewa…

“A gaskiya abun farin ciki ne,idan aka kwatanta shekarun da suka gabata da yanzu.Amma abun laakari anan shine ba yawan mata da suke da madafan iko ba,amma irin ayyuka da zasuyi cikin harkokin siyasar kasar.a zaben daya gabat dai jamiiyyar AKP mai mulkin kasar ta bawa bawa mata dama ,hakan kuma abun yabawa ne.Sai dai kuma adadin matan da suke majalisar har yanzu basu kai yawan wadanda zasu iya yin wani tasiri ba bisa laakari da yawan wakilai da take dasu”.

Profesa Minibas ta jaddada bukatar gudanar da dukkan harkokin siyasan maza tare da matansu kamar yadda wasu kasashe keyi….

“Kamata yayi prime minister Erdogan yayi koyi da tsarin Amurka,na tafiyar da dukkan harkoki da maidakinsa.Amma bai dace ace a majalisa da sauran hukumomi idan ka duba mata kalilan kake gani ba..”