1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata masu bada taimako a Nijar

Abdoulaye Maman Amadou/USUSeptember 13, 2016

Wata kungiya ta mata zalla ta kafa gidauniyar tattara kayan agaji don tallafawa mata da yara kanana a yankin Diffa musamman yan gudun hijira da ma wadanda matsalar Boko Haram ta shafa

https://p.dw.com/p/1K1WJ
Protest gegen Boko Haram in Niamey, Niger
Hoto: AFP/Getty Images/B. Hama

Babban burin da sabuwar gidauniyar mai suna SUTURA ta ke son cimma da kungiyar mata masu masana’antun suka kafa, shi ne na ganin mata masu abin hannunsu da ke manya-manyan birane ciki har da Yamai, sun dauki nauyin 'yan uwansu mata da yara kanana da ke cikin wani mawuyacin hali a yankin Diffa. Farawa daga 'yan gudun hijira har izuwa ga mata na gida da wadanda aka tarar da su, tun daman a cikin wani hali na talauci da karancin cimaka. Hajiya Mariama Daouda Coulbaly, ita ce sakatariyar kungiyar matan masu masana’antu na jamhuriyar Nijar.

Tace "Da 'yan Boko Haram suka zo, mata haka suke fita babu kaya su baro gidajensu. Kenan babu wani tallafin da ya wuce na dan uwanka ya baka abin shi, ya fi kwanciyar hankali. Mun lura kuma sutura ita ce kan gaba. Yau shekaru uku yankin na cikin matsala, don shi ya sa muka ce a tattara masu kayan, idan an tattara sai mu baiwa wadanda in aka basu za su kai kayan gare su"

A cewar Hajiya Dela Mohamed, daya daga cikin matan a Diffa, matan yankin da ma 'yan gudun hijra na cikin wani mawuyacin hali. Abinda yakai su ga yin karo-karo mai taro mai sisi, dama tattara kayan sakawa a jiki don aikawa a yankin, a wani mataki na nuna cewar ciwon ya mace na ya mace ne.

"Matan nan da suka gudo suka zo ba su fita da komai ba kuma wasu daga riga guda wasu kuwa ko takalmi basu da, suka baro gidajensu haka suka zo ba mun ce sai sabbin kaya ba a’a, tsoffin kaya ma suna sakawa, don haka muke so wanda mutane ba sa so sune muke hadawa, kuma mu daga nan sai mu tattara mu dauka mu aikewa wadanda suke can, sai su rinka bin daji-daji suna rarrabawa"

Daya daga cikin matan da ke wakiltar 'yan yankin na Diffa Mme Jibbo Halima Hassane, ta shaida wa tashar DW yanda ta ji da wannan sabuwar gidauniya.

"Akwai matan da suke da juna biyu sun haifu bisa hanyar Diffa zuwa Gingimi,, mutane sun tafiyar kafa, ga shi kuma yankin akwai zafin gaske. Muna son takalmi tunda dig´ffa yanki ne mai rairai akwai zafin rana muna son yan wandnan yara da yan rigunan yara hakan kuma muna son tsoffin tufafi ba wai sai sabbi ba muna wankewa duk mai tausayi ya taimaka. Na ji dadin da ba'a mislitawa ko kadan, kai har muryata ta mutu".

Gidauniyar dai an bude ta ne da wa’adin makwanni uku, ko da yake rahotanni sun ce an kara dagawa har zuwa wasu 'yan watanni. Gwamnatin jamhuriyar Nijar dai ta bakin minisatar kyautata rayuwar al’umma, ta yaba wa matakin da matan suka dauka. Inda ta yi kira ga yan kwangila da su dauki nauyin sufurin kayayakin da matan za su tara, don isar da su a hannun mabukata.

Niger Bevölkerungswachstum Frau mit Kindern
Hoto: Getty Images/AFP/O. Omirin